Ogan tsohon dan jami’yyar ‘National Movement party’ MHP da ke kawance da jami’yyar AK / Hoto: TRTworld

Sinan Ogan dan kimanin shekara 56, ya shiga fagen siyasa daga jam’iyyar MHP a shekarar 2011 inda ya rike matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar a garinsa da ke Igdir, yankin da ke lardin gabashin Anatoliya wanda ke da yawan al’umma ‘yan Azerbaijan.

Sinan Ogan, malami a harshen Azerbaijan na Turkiyya ya tsaya takarar shugabancin kasar karkashin inuwar jam’iyyar kawance ta ATA a zaben da ke tafe a watan Mayu.

Ya samu goyan bayan sama da mutum 100,000, adadin da doka ta ba da damar a tanada don tsayar da dan takarar shugaban kasa.

Jam’iyyar kawance ta ATA na daga cikin gamayyar jam'iyyu hudun da suka mara wa Ogan baya, Jam’iyyar Zafer da Jam’yyar Memleket da Jam’iyyar Kawance ta Turkiyya, wadanda aka fi saninsu da masu ra’ayin kishin kasa.

Ko da yake Jam’iyyar ATA ba ta yi fice ba kamar sauran manyan jam’iyyun kawance na siyasa biyu da ke kan gaba.

Duka jam’iyyun kawancen za su fafata da juna a ranar 14 ga watan Mayu a zaben neman kujerun ‘yan majalisun dokoki da ta shugaban kasa.

Da farko dai, yana da kyakkyawar alaka da Devlet Bahceli, shugaban jam’iyyar MHP amma bayan da Bahceli ya goyi bayan tsare-tsaren Erdogan bayan zaben watan Nuwamba na 2015, Ogan ya shiga cikin sauran masu kishin kasa don adawa da shugabancinsa.

Siyasar Hamayya

Bahceli da Erdogan ba su kasance cikin wani kawancen siyasa ba kafin 2015 lokacin da Turkiyya ta gudanar da zaben gama gari karo na biyu, bayan gaza samun adadin kuri’un da zai bai wa dan takara damar samun nasara a karon farko.

Sai dai bayan da Jam'iyyar AK ta lashe zaben watan Nuwamba wanda ya biyo bayan rushewar tsarin warware rikicin Turkiyya, matakin da Bahceli ya yi adawa da shi, sai aka samu ci gaba a kawance tsakanin jam'iyyar MHP ta Bahceli wacce ta kasance a tsakiya wajen nuna kishin Turkiyya fiye da shekara 50 kenan.

Duk da haka, wasu 'yan siyasa masu kishin kasa kamar Sinan Ogan da Meral Akesener da Umit Ozdag da kuma Koray Aydin duka mambobin jam’iyyar MHP ne kafin su kafa tasu jam’iyyar suna adawa da kawancen Bahceli da Erdogan.

Daga karshe wadannan ‘yan siyasan sun hade a matsayin jam’iyyar adawa da dadadden shugabancin Bahceli.

Shugaban jam'iyyar Nasara Umit Ozdag daga hannu hagu, shugabar jam'iyyar IYI Meral Aksener a tsakiya  da Sinan Ogan dan takarar jam'iyyar kawance ta ATA / Hoto: AA

A watan Yunin 2016, abokan adawar Bahceli, ciki har da Ogan, suka kira wani taro da ke cike da ce-ce-ku-ce don sauya kundin tsarin mulkin jam’iyyar MHP, duk da rashin amincewa da shugabannin jam’iyyar suka yi.

Sun yi hakan ne da nufin korar Bahceli daga mukamin shugabanci, amma saboda rashin jituwar cikin gida a karshe dai taron watan Yunin ya kare ne a kotu.

Taron Jam’iyyar da aka shirya yi a watan Yuli bai yiwu ba, kotu ta yi watsi da matakin sauya kundin tsarin mulkin Jam’iyyar MHP kuma Bahceli ya ci gaba da rike mukaminsa.

Watanni bayan hakan, Aksener da magoya bayanta suka raba gari da MHP sai suka kafa jam’iyyar IYI a shekarar 2017.

Amma Ogan ya ci gaba da zama a MHP duk da an kore shi har sau biyu bisa zargin aikata ayyukan da suka ci karo da jam’iyyar.

Da farko kotu ta soke karar tasa saboda ‘’bai sauya sheka zuwa ko wacce jam’iyya ba. Kuma bai kafa wata sabuwar jam’iyya ba’’kamar yadda shafin intanet na Ogan ya wallafa.

Ya bayyana cewa zai ci gaba da yin biyayya ga jam’iyyarsa da gwagwarmayarta."

Tun shekarar 2017 Ogan bai hada wata alaka da kowace jam’iyya ba kuma a zaben da ke tafe zai tsaya a matsayin dan takara mai cin gashin kansa, duk da cewa jam’iyyar kawance ta ATA karkashin jagorancin Ozgag ta tsayar da shi a matsayin dan takararta na shugaban kasa.

A yayin wani taron manema labarai, ‘yan jaridun Turkiyya sun tambayi Ogan wane dan takara zai mara wa baya idan zaben ya shiga zagaye na biyu tsakanin Erdogan da Kilicdaroglu, idan har babu dan takarar da ya samu kuri’u sama da kashi 50 a zagayen farko.

“Za mu duba matsayinsu da kuma kwarewarsu. Za mu duba halin da ake ciki na alaka da ta'addanci da neman taimako daga ta'addanci. Za mu yanke shawara cikin hankali.

"Hankali ya nuna mana cewa watakila ba za mu iya yin alkawarin samar da Aljanna ba, amma lokaci ya yi da za mu rufe kofofin wuta,” amsar da Ogan ya bayar kenan.

Sinan Ogan zai tsaya takara karkashin jam'iyyar kawance ta ATA da Umit Ozdag ke jagoranta /Hoto: AA

Asalin Ogan

Dan siyasar mai kishin kasa ya kammala karatunsa daga Jami’ar Marmara a1989, inda ya samu digiri a fannin kasuwanci, ya kuma kammala karatun digirinsa na biyu a fannin dokar kudi da banki, duk daga jami’a daya a 1992.

Daga baya a shekarar 2009 ya kammala karatun digirinsa na uku a Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa da ke jihar Moscow ta kasar Rasha, MGIMO.

Tsakanin wannan shekarar zuwa ta 2000, ya yi aiki a matsayin malami a Cibiyar Nazarin Duniya ta Turkic ta Azerbaijan, a cewar shafinsa na intanet. A lokaci guda kuma ya jagoranci ofishin Hukumar Hadin Kan Turkiyya, TIK, da ke Azabaijan.

A shekarar 2000, ya yi aiki a Cibiyar Bincike ta Nahiyar Turai da Asiya (ASAM), inda ya jagoranci sashen bincike na Rasha-Ukraine.

A 2004 ya kafa cibiyar bincikensa mai suna Cibiyar Binciken Dabaru ta Turkiyya TURKSAM, wacce ke ci gaba da aiki har yanzu.

Bayan ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar MHP a shekarar 2011, ya kasance mamba a kungiyoyin kawance na 'yan majalisun dokokin Albaniya da Turkiyya da kuma Nijeriya.

A lokacin shugabancinsa, Ogan ya kuma yi aiki a matsayin Babban Sakataren Kungiyar Kawance ta 'Yan Majalisar Turkiyya da Azerbaijan.

TRT World