Emine Erdogan ta yi gargaɗi game da yanayin da ake ciki a halin yanzu wanda ke barazana da bil'adama da sauran halittu tare da kai su zuwa ga halaka ta har abada. / Photo: AA

Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira da a dauki matakin gaggawa don kare duniya tare da tabbatar da ɗorewar makoma ga kowa da kowa yayin jawabinta a wani taron koli na sauyin yanayi a Dubai.

Da take jawabi a ranar Talata a taron Shirin Ci gaba mai Ɗorewa na 2045: Zayyana Makomar shirin Duniyarmu a matsayin wani bangare na taron koli na gwamnatocin duniya a Dubai, Emine Erdogan ta jaddada cewa akwai bukatar samun manufa daya tsakanin mutane daga kasashe daban-daban da mabambantan al'adu da addinai don kare duniya da samar da duniya mai ɗorewa ga al'ummomi masu zuwa.

Ta yi gargaɗi game da yanayin da ake ciki a halin yanzu wanda ke barazana da bil'adama da sauran halittu tare da kai su zuwa ga halaka ta har abada.

Ta kuma jaddada bukatar kowa da kowa ya bayar da tasa gudunmawa don rage tasirin sauyin yanayi a kan muhalli tare da bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe domin tunkarar kalubalen duniya kamar matsalar yanayi da gurbatar yanayi.

Ta bayyana irin gudunmawar da Turkiyya ta bayar, ciki har da shirinr Zero Waste da hadin gwiwa da sauran kasashe.

Erdogan ya kuma yi magana game da muhimmancin ilimi da wayar da kan jama'a wajen inganta ci gaba mai ɗorewa. Ta ce akwai bukatar a bai wa matasa karfin gwuiwa wajen daukar matakai da kawo sauyi.

Makomar duniyar ta dogara kan ayyukanmu, in ji ta.

TRT World