Yarjejeniyar ta kunshi hada hannu waje guda don tabbatar da cigaba da kuma amfani da albarkatun mai da iskar gas na Somaliya. Hoto: Ma'aikatar Makamashi da Albarkatun Kasa ta Turkiyya.

Turkiyya da Somaliya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatocinsu domin inganta haɗin gwiwa a fannin haƙar man fetur da iskar gas a mashigar ruwa ta tekun Somaliya.

An dai tsara yarjejeniyar ne a gaban Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar da kuma Ministan Albarkatun Man Fetur da Ma'adinai na Somaliya Abdirizak Omar Mohamed.

A ƙarƙashin wannan yarjejeniya, za a gudanar da ƙoƙarin haɗin gwiwa don amfani da albarkatun ƙasar Somaliya don amfanin al'ummarta, in ji Ministan na Turkiyya a wani saƙo da ya wallafa a shafin X a ranar Alhamis.

Yarjejeniyar ta nuna alkawarin shiga ayyukan haɗin gwiwa da za su taimaka wajen haɓakawa da amfani da albarkatun man fetur da iskar gas na Somaliya.

Bayraktar ya ƙara da cewa, wannan mataki da ya dace, wani ɓangare ne na babban burin Turkiyya na ƙarfafa kasancewarta a yankin Afirka ta hanyar sabbin hanyoyin hadin gwiwa a fannin makamashi, da cin moriyar juna da hadin gwiwa a yankin.

Yarjejeniya mai cike da tarihi

Yarjejeniyar hako albarkatun mai da iskar gas din na zuwa ne makonni biyu bayan majalisar dokokin Somalia ta fitar da wata yarjejeniya ta hadin kan tsaro da tattalin arziki, yarjejeniyar da ta baiwa Turkiyya wa'adin shekara 10 don samar da tsaro a tekun Somalia.

Yarjejeniya ba iyakacin tekun Somaliya ta shafa kawai ba, ta kuma samar da yanayin da za a kafa sansanin sojin ruwa don bayar da tsaro ga yankin Kahon Afirka.

Alakar Turkiyya da Somaliya ta zama daya daga abubuwan da ke fayyace manufofin Turkiyya a Afirka.

A 2011, Shugaban kasar Turkiyya, a lokacin yana Firaminista ya zama shugaban da ba na Afirka ba na farko da ya ziyarci Somalia a cikin shekaru 20.

Tun wannan lokaci, ya ziyarci kasar a lokuta daban-daban kuma ya karbi bakuncin shugabannin Somalia a Turkiyya.

TRT World