Za a gudanar da Taro Karo na Uku na Kasashen Kudancin Caucasia a Istanbul, Turkiyya, zai mayar da hankali wajen dabbaka zaman lafiya, cigaban tattalin arziki da kusantar juna a yankin ta hanyar hadin kai mai karfi.
Taron, da za a gudanar ranar Juma'a kuma Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ne zai karbi bakuncinsa, zai tattara manyan jami'an diflomasiyya daga Azerbaijan da Armenia da Iran da Rasha.
Ministan Harkokin Wajen Azerbaijan Ceyhun Bayramov, Ararat Mirzoyan daga Armenia, Abbas Araghchi na Iran da Sergey Lavrov na Rasha na daga cikin mahalarta taron.
Ana sa ran Minista Fidan zai yi karin haske kan kokarin Turkiyya na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kudancin Caucasia kuma zai jaddada muhimmancin mallakin yankin wajen wareware rikice-rikice.
Akwai yiwuwar kuma zai sake jaddada goyon bayan Turkiyya ga tattaunawar zaman lafiya da ake ci gaba da yi tsakanin Azerbaijan da Armenia, sannan ya ambaci batun sasantawa tsakanin Turkiyya da Armenia.
Taron na da manufar gina aminci ta hanyar hadin kan tattalin arziki, musamman a bangarorin kusantar juna da cudanyar kasuwanci.
Kazalika, an shirya tattaunawar musamman tsakanin ministocin harkokin wajen, da kuma walima da Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai jagoranta.
Ana sa ran taron zai karkare da amincewa da Sanarwar Hadin Gwiwa, yana mai karfafa muhimancin warware rikici ta hanyar tattaunawa, girmama iyakoki da 'yancin mulkin kasashe, da hadin kan tattalin arzikin yankin.
Tsarin “3+3”
An kafa Kungiyar Hadin Kasashen Kudancin Caucasia bayan Yakin Karabakh na Biyu a 2020, karkashin jagorancin Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev da nufin samar da wata inuwa ta warware matsalolin yankin da karfafa hadin kai.
An gudanar da taron farko a watan Disamban 2021 a Moscow, inda aka gudanar da na biyu a Tehran a ranar 23 ga Oktoban 2023 da sigar "3+3".
Kungiyar ta kunshi kasashen Azerbaijan, Armenia, Georgia, Iran, Rasha da Turkiyya.