''Huldar 'yan uwantaka'' da ke tsakanin Shugaba  Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya da takwaransa Ismail Omar Guelleh ta kasance abin da ke ciyar da huldar kasashen gaba / Hoto: AA

Turkiyya da Djibouti na bikin cika shekara goma da bude ofishin jakadancin Tukiyya a Djibouti da kuma fara jigilar matafiya da kamfanin jiragen saman Turkiyya, Turkish Airlines ke yi zuwa kasar da ke yankin Kusuwar Afirka.

Cikin wani sakon bidiyo da ya yi a wani zaman bude baki na musamman a Djibouti, a matsayin wani bangare na bikin zagayowar ranar, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya ce Turkiyya na aiki don habaka zuba jarinta a Djibouti.

Ya ce ana fata jarin ya dara dala biliyan daya tare da kai huldar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa "wani mataki na musamman.''

Mista Çavuşoğlu ya gode wa Djibouti da hadin kan da ta bayar a lokacin girgizar kasar da ta afka wa kudancin Turkiyya a watan Fabrairu, wadda ta kashe mutum sama da 50,000 ta kuma shafi mutum fiye da miliyan biyu.

Ofishin jakadancin Turkiyya da kuma kamfanin jiragen sama na Turkish Airlines ne suka shirya taron buda baki don nuna farin ciki game da huldar da ke tsakanin kasashen / Hoto: Türkish Embassy, Djibouti

Ya kuma jajanta wa gwamnati da kuma mutanen Djibouti game da mutuwar dalibai biyar 'yan Djibouti a bala'in.

Kamfanin jiragen Turkiyya, Turkish Airlines, tare da ofishin jakadancin Turkiyya a birnin Djibouti ne suka shirya taron buda bakin.

Jakadan Turkiyya a Djibouti, Cenk Uraz ya ce a yanzu Turkiyya na daga cikin manyan abokan cinikayyar Djibouti.

''A shekarar da ta gabata, yawan cinikayyar da ke tsakaninmu ta zarce na da, inda ya wuce dala miliyan 500.

"A halin yanzu Turkiyya na daga daga cikin manyan abokan cinikayyar Djibouti,'' kamar yadda ya shaida wa taron da ya samu halartar ministocin gwamnatin Djibouti shida.

Turkiyya ta kaddamar da ofishin jakadancinta a Djibouti a shekarar 2013, shekara daya bayan kasar ta Gabashin Afirka ta bude ofishin jakadancinta a Ankara.

Jakadan Turkiyya Cenk Uraz ya ce duk da cewar ‘’shekara 10 kawai aka yi bayan an bude ofishin jakadancinmu, huldarmu da Djibouti ta cigaba sosai a dukkan fannoni a kan girmama juna da hadin kai.’’

Jami'an diflomasiyyar Turkiyya a Djibouti na son a kara hulda tsakanin kasashen biyu /Hoto: Turkish Embassy, Djibouti

Ya ce wasu daga cikin muhimman fannonin da hulda ke dada karuwa tsakanin kasashen biyu sun hada da kasuwanci da ilimi, inda daliban Djibouti 1400 ke karatu a Turkiyya tare da bai wa kwararrun Djiboutia horo a fannoni daban-daban.

Jakadan Turkiyyan ya ce dangantaka tsakanin Turkiyya da Djibouti an gina ta ne "kan fahimta ta cigaban kasashen biyu."

Mista Uraz ya ce kasarsa na kokarin habaka huldarta da nahiyar Afirka gaba daya, yana mai cewa: ''A yau, da jiragensa 411, kamfanin jiragen Turkiyya, Turkish Airlines ya fi kowane kamfani wuraren zuwa, saboda yana zuwa wurare 343 a kasashe129. Wannan ya hada da birane 60 a Afrika.’’

A cewar jami'in diflomasiyyar Turkiyyan, "huldar 'yan'uwantaka" tsakanin Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya da takwaransa na Djibouti Ismail Omar Guelleh, da kuma ‘’dangantaka ta kut-da-kut’’ tsakanin mutanen kasashen biyu su suke kara ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu gaba.

TRT Afrika da abokan hulda