Fahrettin Altun ya karyata wasu labarai da ke cewa Shugaba Erdogan ya samu bugun zuciya. Hoto/AA

Gwamnatin Turkiyya ta yi watsi da labarai "marasa hujja" game da koshin lafiyar shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan.

"Mun yi watsi da daukacin ikirarin da aka yi game da koshin lafiyar Shugaba @RTErdogan. Gobe shugaban kasar zai halarci taron bude tashar nukilyar ta [ Akkuyu Nuclear Power Plant] ta manhajar bidiyo," a cewar daraktan sadarwa na kasar Fahrettin Altun a sakon da ya wallafa a Twitter ranar Laraba.

"Babu wani labarin kanzon-kurege da zai sa al'ummar Turkiyya su gaza tsayawa tare da shugabansu kuma Shugaba @RTErdogan da jam'iyyar AK [Justice and Development] sun kama hanyar lashe zaben 14 ga watan Mayu," in ji Altun.

Ma'aikatar watsa labarai ta yi watsi da wasu labaran karya da aka watsa a wasu shafukan sada zumunta da cewa Shugaba Erdogan "ya samu bugun zuciya kuma an kwantar da shi a asibiti".

Putin zai halarci taron

Tashar nukiliya ta Akkuyu da ke lardin Mersin na kudancin kasar ita ce ta farko a Turkiyya da za a kaddamar, kuma tana da karfin megawat 4,800 da kuma na'urorin da ke aiki da ita guda hudu.

An soma aikin gina tashar ne a 2010 a wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin Turkiyya da Rasha, inda ake sa ran tashar gaba dayanta za ta yi aiki a 2025.

Kazalika shugaban Rasha Vladimir Putin zai halarci bikin kaddamar da tashar ta manhajar bidiyo, a cewar kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov a sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

AA