Turkiyya ta sha alwashin kawo ƙarshen ta'addanci, tana mai jaddada cewa ba za ta ɗaga ƙafa ga ƙungiyoyin ta'addanci a makomar "yankinmu" ba.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, Majalisar Tsaron Ƙasa ta Turkiyya, wadda ta gana a Ofishin Shugaban Ƙasa da ke Ankara ƙarƙashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, ta ce ba za ta sassauta wa "ƙungiyoyin ta'addanci da masu goyon bayansu don juya makomar yankinmu ba."
"Muna sanya ido sosai kan hare-haren da ƙungiyoyin ta'addanci na PKK/PYD/YPG suke kai wa ƴan ƙasarmu da ke zaune a ƙasashen turai," in ji sanarwar.
Majalisar Tsaron Ƙasar ta yi kira ga dukkan mutanen da ke "goyon bayan ƙungiyoyin yan ta'adda" su yi gaggawar yanke "hulɗa da ta'addanci."
A shekaru kusan 40 da ƙungiyar PKK – wadda Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci – ta kwashe tana kai hare-hare ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da mata da ƙananan yara da jarirai. YPG shi ne reshen ƙungiyar PKK da ke ƙasar Syria.