Migrants

Jami’an Tsaron Tekun Turkiyya sun kubutar da bakin haure 132 bayan da jami’an tsaron Tekun Girka suka kora su zuwa iyakar Turkiyya.

Rundunar Tsaron Tekun Turkiyya ta bayyana cewa an kubutar da bakin haure 85 a gabar tekun gundumar Dikili bayan da jami’an tsaron tekun Girka suka kora su zuwa iyakar tekun Turkiyyan.

Mahukunta sun dauki mataki bayan samun labarin ganin bakin hauren a jiragen ruwan roba uku daban a yankin Foca.

A samamen da aka kai an kubutar da bakin haure 42, wadanda su ma jami’an tsaron tekun Girka ne suka hankada su zuwa iyakar Turkiyya.

Rahotannin da aka samu bayyana an sake tseratar da wasu bakin hauren su 43 a gabar tekun gundumar Dikili.

A gundumar Bodrum ta lardin Mugla ma an sake kubutar da wasu ‘yan gudun hijira ba bisa ka’ida ba su 47 a lokacin da suke kokarin barin Turkiyya ta barauniyar hanya.

TRT World