Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da sako ga duniya kan Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya, inda ya yi karin haske kan cewa a ko yaushe ayyukan Turkiyya za su kasance “kare rayuka da mutuncin dan adam, tare da tsare kasa”.
Ya ce “Turkiyya da a ko yaushe take sauke nauye-nauyen da ke kanta na jibintar al’amuran dan adam da kare hakkin makotaka, na aiki don tabbatar da komawar ‘yan gudun hijira kasashensu bisa radin kansu cikin mutunci da girmamawa."
“Mutane a sassan duniya daban-daban, har ma da yankin da kasarmu take, na shiga mawuyacin halin da ke tilasta musu gudun hijira saboda dalilai na ta’addanci da yaki da yakin basasa da yunwa da karancin cimaka.”
Shugaban na Turkiyya ya jaddada cewa kasarsa ta tsaya tare da wadanda suka gujewa zalunci ba tare da nuna musu bambanci ba.
“Hanyarmu ta tunkarar batun gudun hijira ba bisa ka’ida ba wadda kalubale ne daga duniya baki daya ita ce a kare rayukan mutane da mutuncinsu, tare da samar da tsaron kasarmu.
Kasarmu da ta jima tana kula da wadanda suka gujewa zalunci ba tare da nuna bambanci ba tsawon karni da dama, kuma ta sake nuna wannan dattako a lokacin da yankinta ke fama da rikice-rikice, daga Siriya zuwa Yukren.” Inji Erdogan.
Shugaban ya zayyana hanyar da kasarsa ke bi don karbar ‘yan gudun hijira a matsayin kalubale ga duniya.
Ya ce “Muna adawa da kalaman nuna tsana, yaduwar sabon ra’ayin Nazi, da kuma nuna kyamar Musulunci, wanda ya samo asali daga kasashen Yamma sannan ya yadu zuwa sauran al’ummu kamar wani dafi.
"Muna kallon wannan mummunar dabi’a da ba ta kyale kowa ba, ba ta kyale kowacce al’ada da addini ba a matsayin babbar illa gare mu baki daya.”
“Muna kira ga dukkan bangarori da su kara zage damtse”
Da yake kara haske game da tasirin akidar mulkin mallaka, Shugaba Erdogan ya yi nuni da yadda Tekun Bahar Rum ya zama makabartar mutane da yawa tsawon shekaru.
Ya kara da cewa “tare da takadarin ra’ayin da ke komawa ga mulkin mallaka, ake samun mummunan tasiri a Bahar rum, wanda a baya yake cibiyar wayewa a tarihim a yanzu kuma ya zama makabartar mutane da dama a ‘yan shekarun nan.”
Ya ci gaba da cewa “Mummunan lamarin da ya afku a makon da ya gabata a Tekun Aegean inda daruruwan mutane, mafi yawansu yara kanana suka rasa rayukansu da tsakar rana, ya zama abun kunya da za a iya bayar da misali a yau.”
Ya jaddada muhimmancin da Yarjejeniyar ‘Yan Gudun Hijira da aka sanya hannu a kai a 2018, da Turkiyya ta baiwa gudunmowa ke da shi wajen warware wannan matsala.
Za a iya magance wannan matsala ne idan aka magance abubuwan da ke tilastawa mutane gudun hijirar.
Ya yi kira ga mahukunta da su kara kokarin da suke yi don cika wannan alkawari da suka dauka.
Ya ce ”Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su zage damtse wajen aiwatarwa da aiki da wannan yarjejeniya.”
Shugaba Erdogan ya karkare sakonsa da bayyana fatan cewa Ranar Gudun “Yan Hijira ta Duniya za ta bayar da gudunmowa wajen warware kalubalen da ‘yan gudun hijira ke fuskanta a duniya baki daya.