Kasar Girka ta bayyana "kwarin gwiwarta" ga ci gaban dangantaka da tattaunawa kan siyasa da Turkiyya, a cewar Ministan Harkokin Wajen kasar.
“Mun tsara wasu matakai na ganawa da sake saitawa da kuma karfafa kyakkyawar alaka da Turkiyya,” a cewar George Gerapetritis a wata hira da gidan talabijin na Al Qahera TV na Masar ya yi da shi a ranar 3 ga watan Agusta, wanda ma'aikatar harkokin wajen Girka ta fitar ranar Litinin.
George ya bayyana cewa shi da takwaran aikinsa na Turkiyya Hakan Fidan sun samar da wata hanya ta tattaunawa.
“Abin da muke so mu yi shi ne, mu yi kokarin inganta manufa mai kyau tare da batutuwan da suka dace, kamar kasuwanci da tattalin arziki da kuma kare fararen-hula da yawon bude ido da kuma duk wasu ayyuka da suka shafi ci-gaban kasashenmu baki daya, sannan mu yi aiki kan dangantakarmu," in ji shi.
Sanya iyaka a teku
Gerapetritis ya kafa hujjar cewa sanya iyaka a teku shi ne bambanci mafi girma da ke tsakanin kasashen biyu.
"Muna tunanin mika wannan takaddama ga kotun kasa da kasa da ke Hague," in ji shi.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da firaiministan Girka Kyriakos Mitsotakis sun gana a watan Yuli a yayin taron kungiyar tsaro ta NATO da aka gudanar a birnin Vilnius na kasar Lithuania.
Kazalika taron ya zame wa kasashen biyu wani muhimmin mataki na ci-gaba.
Ana sa ran gudanar da wani sabon zagayen tattaunawa kan muhimman matakan hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Girka a birnin Thessaloniki a wannan kaka.