Turkiyya da kungiyoyin kare hakkin duniya sun sha yin Allah wadai ga haramtaccen matakin da kasar Girka ke dauka na korar bakin haure ba bisa ka'ida ba. / Hoto: AA

Jami'an tsaron gabar Tekun Turkiyya sun ceto bakin-haure sama da 270 da suka saba ka'ida bayan da hukumomin Girka suka kora su yankin ruwan Turkiyya ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwar da ta wallafa a shafinta na intanet, rundunar tsaron gabar tekun Turkiyya ta bayyana cewa, ta ceto bakin-haure 140 wadanda ke tafe ba bisa ka'ida ba a cikin Tekun Aegean, bayan mayar da kwale-kwalensu da hukumomin Girka na yankin Bodrum da Dalaman suka yi zuwa Tekun Birnin Mugla.

Kazalika, sashen jami'an tsaron gabar tekun sun kubutar da jumullar bakin-haure 57, daga cikin wani kwale-kwalen roba a gabar tekun yankunan Dikili da Cesme da ke yammacin lardin Izmir.

An kuma ceto wasu karin bakin-hauren 67, wadanda jami'an tsaron Tekun Girka suka kora su zuwa ruwan Turkiyya na yankin Kusadasi da Didim da ke lardin Aydin na kasar Turkiyyar.

A wani bangaren na daban, tawagar jami'an tsaron gabar tekun sun ceto wasu bakin- haure 10, wadanda ke tafiya cikin wani kwale-kwalen da ke da matsala a gabar tekun gundumar Gomec da ke lardin Balikesir.

Turkiyya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na duniya sun sha yin Allah wadai da haramtaccen matakin kasar Girka na korar bakin-haure wadanda ke tafe ba bisa ka'ida ba.

Sun ce hakan ya saba wa ka'idojin jin-kai da dokokin kasashen duniya, suna masu cewa yin hakan na kara jefa rayuwar bakin-haure masu rauni ciki har da mata da kananan yara cikin hatsari

TRT World