Turkiyya ba za ta tattauna kan duk wani aiki da ya shafi makamashi da Isra'ila ba, ba tare da an tsagaita wuta a Zirin Gaza ba, domin hakan zai zama tamkar rashin mutunta 'yan uwanmu Falasdinawa da ke fuskantar zalunci, a cewar Ministan Makamashin kasar.
"A cikin wannan mummunan yanayin ukuba da take hakkin dan'adam, zai zama tamkar rashin darajta rai ne ga 'yan uwanmu Falasdinawa idan muka tattauna kan kowane irin aiki da Isra'ila," in ji Ministan Makamashi da Albarkatun Kasa na Turkiyya Alparslan Bayraktar a ranar Talata a hira da wani gidan talabijin mai zaman kansa.
"Bayan irin zalunci da rashin tausayi da Isra'ila ke nunawa, aiki daya tilo da za mu iya magana a kai a yanzu shi ne yadda za mu sake maido da wutar lantarki a Gaza," in ji shi, yana mai cewa rayuwa ta tsaya cak a yankin sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.
“Mun aika da injinan janareto. Suna can Mashigar Rafah,” a cewar Ministan.
“Ta yaya za mu iya ba da gudunmawarmu a can da na’urorin samar da wutar lantarki da jirgin ruwa na lantarki na tafi-da-gidanka da ke shawagi a kan ruwa? Za mu iya maido wa da wadannan mutanen rayuwarsu ta yau da kullun amma abu ne mai kamar wuya a iya tattaunawa a kan wani abu ba tare da an tsagaita bude wuta."
Bayraktar ya jaddada cewa Falasdinu na da matsayi na musamman a zuciyarsa, yana mai cewa an tattauna kan ayyukan samar da wutar lantarki a kasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya a wata yarjejeniyar da aka kulla da bangaren Isra'ila bayan shekarar 2016.
An kashe sama da Falasdinawa 10,000
Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama da ta kasa a Gaza bayan wani harin ba-zata da kungiyar Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke yi a Gaza tun daga lokacin ya kai mutum 10,328.
Daga cikin mutanen da aka kashe akwai yara 4,237 da mata 2,719, a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Ashraf al-Qudra a wani taron manema labarai ranar Talata.
Kazalika mutane fiye da 25,956 ne suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai a Zirin Gaza.
A daidai lokacin da adadin mutanen da suka mutu ke ci gaba da karuwa, kayayyakin masarufi na ci gaba da karewa a Gaza bayan "cikakkiyar kawanya" da Isra'ila ta yi wa yankin inda ta kusan dakatar da kai duk wani agaji na jinkai.