Turkiyya ta bayyana alhinin ta dangane da wani mummunan hatsarin jirgin saman fasinja da ya afku a kusa da birnin Aktau na kasar Kazakhstan.
Jirgin dai yana kan hanyarsa daga Baku zuwa Grozny ne lokacin da wannan mummunan lamari ya faru a ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da fatan Allah ya jikan wadanda suka rasu, tare da yin addu'ar samun sauki ga wadanda suka jikkata cikin gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa "A shirye muke mu ba 'yan'uwanmu na Azabaijan da Kazakhstan duk wani tallafi da zai taimaka a wannan mawuyacin lokaci."
A jiya Laraba ne wani jirgin saman kasar Azerbaijan dauke da mutum 67 da ya taso daga Baku babban birnin kasar Azabaijan zuwa Grozny a Jamhuriyar Chechen ta kasar Rasha ya yi hatsari a kusa da birnin Aktau na kasar Kazakhstan.
Ma'aikatar agajin gaggawa ta kasar Kazakhstan ta sanar da cewa akwai mutum 25 da suka tsira da rayukansu.
A cewar ma'aikatar, fasinjoji 62 da ma'aikatan jirgin biyar ne ke cikin jirgin mai lamba 8432, wanda ya kama da wuta bayan hadarin, inda ta kara da cewa masu bayar da agajin gaggawa sun yi kokarin kashe wutar.
Ma'aikatar ta ce "Jimillar mutum 67 ne ke cikin jirgin, ciki har da ma'aikatan jirgin guda biyar ... Ba da agajin ya hada da ma'aikata 150 da kuma sassan kula da lafiya na gaggawa 45. A halin yanzu ana tantance sunayen fasinjoji," in ji ma'aikatar.
Da farko ma'aikatar ta ba da rahoton wasu mutum 25 da suka tsira da rayukansu, amma daga baya ta sabunta alkaluman, inda ta ce mutum 28 ne tsira daga hadarin, ciki har da yara biyu.