Jami'an tsaron Turkiyya sun "kawar da" akalla 'yan ta'adda 57 na kungiyar PKK a arewacin Iraki da Syria a awanni 24 da suka gabata, in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Tsaron kasar ta fitar.
"A awanni 24 da suka gabata, adadin 'yan ta'adda da aka kawar ya karu zuwa 57. Muna ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa," a cewar sanarwar wadda aka fitar ranar Asabar.
Ta kara da cewa an kawar da 'yan ta'adda 48 a arewacin Iraki, yayin da aka kawar da tara a arewacin Syria.
A wata sanarwa ta daban da ta wallafa a shafin X, ma'aikatar ta ce wasu hare-hare na sama da jiragen yakin Turkiyya suka kai sun lalata maboya 25 ta 'yan ta'addan a arewacin Syria da lardunan Metina, Hakurk, da Qandil na araewacin Iraki, inda aka "kawar da" 'yan ta'adda da dama.
An fitar da sanarwar ce bayan manyan jami'an gwamnatin Turkiyya sun gudanar da taro kan sha'anin tsaro a Istanbul ranar Asabar, kwana guda bayan 'yan ta'adda na PKK sun kashe sojojin Turkiyya tara a arewacin Iraki.
"Za mu ci gaba da kai hari kan 'yan ta'adda har sai mun kawar da dukkansu da kuma maboyarsu a Iraki da Syria," a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Sadarwa ta Turkiyya ta fitar bayan kammala taro a Istanbul wanda Shugaba Reecep Tayyip Erdogan ya jagoranta.