Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kassarawa" don nufin an kashe ko kama dan ta'adda ko ya mika wuya. / Hoto: AA Archive

Dakarun leken asirin Turkiyya sun kawar da wata babbar jagorar 'yan ta'addar PKK/KCK a arewacin Iraki, in ji majiyoyin tsaro.

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) sun kama Rojda Bilen da ake wa lakabi da Bisng Brusk, a wani farmakin yaki da ta'addanci da aka kai a kan iyaka a yankin Sulaymaniya na kasar Iraki, majiyar ta sanar da hakan a ranar Talata.

Bilen ne babban jami'in kungiyar ta'addar a Sulaimaniyah, in ji majiyar da ta nemi a boye sunanta saboda rashin izinin yin magana da manema labarai.

Majiyar ta kara da cewa ta shiga kungiyar ta'adda ta PKK a 2011 kuma tana jerin shudi na sunayen 'yan ta'addar da ake nema ruwa a jallo.

An kasa jerin sunayen 'yan ta'addar da ake nema ruwa a jallo da kaloli biyar, inda Ja ya zama a kan gba,sai Shudi, Kore, Rawaya da Ruwan Toka,

A cikin sama da shekaru 35 na ta'addancin da ta yi kan Turkiyya, ƙungiyar ta'adda ta PKK - wacce Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka sanya a jerin ƙungiyoyin 'yan ta'adda - ta ɗauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000 da suka haɗa da mata, yara da jarirai. YPG shi ne reshen ƙungiyar na Siriya.

'Yan ta'addar PKK na buya a arewacin Iraki ina suke kai hare-hare iyakar Turkiyya.

Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar "kawarwa" don nufin an kashe ko kama dan ta'adda ko ya mia wuya

TRT World