Turkiyya na yaki da 'yan ta'addar a ware na PKK a ciki da wajen kasar/ Hoto: TRT World

Jami’an tsaro sun kassara kusan ‘yan ta’addar PKK 50 a arewacin Siriya da Iraki, in ji Ministan Tsaron Turkiyya Hulusi Akar.

A yayin wani biki a yankin Kayseri na tsakiyar Anatoliya, Minista Akar ya bayyana cewa “An kassara ‘yan ta’adda takwas a daren jiya. Adadin ya kawo yawan ‘yan ta’adda da aka kassara a kwanaki 10 da suka gabata zuwa kusan 50.

Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar kassarawa da nufin an kama ko kashe dan ta'adda ko kuma sun mika wuya.

Da yake tunatarwa kan nasarorin da jami’an sojin Turkiyya suke samu wajen yaki da ta’addanci, Akar ya kuma jaddada yadda ‘yan ta’adda ke yi wa Turkiyya barazana.

Ya ce “Suna kokarin yin barazana ga hadin kai da taimakon juna da karfin mulki da tsaronmu. Tare da ayyukan yaki da ta’addanci da ake yi, tun daga watan 24 ga watan Yuni 2015 zuwa yau, an kassara ‘yan ta’adda 37,793.”

Ya yi alkawarin za su ci gaba da yaki da ta’addanci har sai sun samar da tsaro a iyakokin Turkiyya.

Tsawon shekaru sama da 35 da suka gabata, PKK da kasashen Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta’adda, na aikata ta’addanci a Turkiyya inda ta kashe sama da mutum 40,000 da suka hada da mata da yara kanana.

TRT World