Jami’an Tsaron Turkiyya sun kama ƴan ta’adda 48 a wani samame da suke kaiwa na daƙile ƴan ta’addan Daesh waɗanda suka kai hari kan Cocin Santa Maria da ke Santambul, kamar yadda ministan cikin gida na ƙasar ya tabbatar.
“A samamen da aka kai kan ƙungiyar ƴan ta’adda ta Daesh, an kama mutum 48 waɗanda ake zargi, musamman waɗanda suke da alaƙa da harin da aka kai 28 ga watan Janairu a Cocin Santa Maria da ke Santambul, inda aka kashe mutum guda,” kamar yadda Ali Yerlikaya ya bayyana a shafinsa na X a ranar Asabar.
Samamen da aka kai mai suna Bozdogan-21, yan sandan Santambul da na Ankara ne suka gudanar da shi da kuma haɗin gwiwar jami’an leƙen asiri.
A lokacin samamen, jami’an tsaron daƙile ayyukan ta’addanci na Santambul sun kama mutum 30 waɗanda ake zargin suna da alaƙa da harin da aka kai Cocin Santa Maria sannan sauran mutum 18 ɗin masu alaƙa da Daesh ƴan sandan Ankara ne suka kama su.
Harin da aka kai a cocin ta Santambul a watan Janairu ƙungiyar ta’addanci ta Daesh ce ta ɗauki nauyin kai shi.
Harin ya yi sanadin mutuwar Tuncer Cihan mai shekara 52.