Turkiyya ba ta amince da mamayar yankin Crimea da Rasha ke yi ba, kuma tana ci gaba da kallon yunkurin a matsayin rashin halacci, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan.
"Tabbatar da tsaro da walwalar danginmu na Tatar da ke Crimea, wadanda su ne 'yan asalin Crimea, na daga cikin abubuwan da muka bai wa fifiko," in ji Shugaba Erdogan, a wani sakon bidiyo da ya aike ga Babban Taron Crimean Karo na Uku da ake gudanarwa a Kiev, babban birnin Yukren.
Erdogan ya ce kawo karshen yakin Rasha da Yukren tare da dawo da zaman lafiya a yankin Tekun Maliya, zai kawo sauki ba wai ga yankin ba, ga duniya baki daya.
Ya kara da cewa "Kuma muna sake jaddada matsayarmu ta kare martabar 'yancin iyakokin Yukren da karfin mulkin kanta. Mun sha nanata cewa Crimea wani bangare ne na Yukren, har a Majalisar Dinkin Duniya mun bayyana haka."
Turkiyya ta bayyana imaninta na ganin an kawo karshen yakin da aka fara watanni 18 da suka gabata tare da samar da zaman lafiya na din-din-din.
"Muna yin babban kokari wajen barin kofofinmu a bude don tattaunawar da z ata kawo dakatar da zubar da jini, sannan a shirya bangarorin su zauna a teburin sulhu."
Yarjejeniyar Jigilar Hatsi ta Tekun Maliya
Shugaba Erdogan ya kuma bayyana cewa Turkiyya na ci gaba da kokarin ganin an dawo da aiki da Yarjejeniyar Jigilar Hatsi ta Tekun Maliya, kuma a yayin hakan, Ankara ta yi amanna da nisantar matakan da za su ta'azzara rikicin yankin.
A ranar 17 ga Yulin wannan shekarar Rasha ta dakatar da aiki da yarjejeniyar.
A watan Yulin 2022 aka sanya hannu kan yarjejeniyar bayan da Turkiyya ta shiga tsakani don ganin an dawo da fitar da hatsi daga tashoshin jiragen ruwa uku na Yukren da Rasha ta sanya wa shinge sakamakon yakin da suka fara a watan Fabrairun shekarar.
Erdogan ya kuma jaddada cewa suna sa ran za a saki Nariman Dzhelyal, mataimakin shugaban majalisar Tatar a Crimea, da sauran 'yan Tatar da Rasha ta kama a 2021.
Dandalin Crimea wata kafa ce ta kasa da kasa da ke Yukren mai manufar janyo hankalin duniya ga yadda Rasha ta mamayi Crimea tun 2014.