Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika sabbin gidaje da aka gina a kauyuka goma a yayin da gwamnati ta soma gagarumin aikin sake gina gidaje ga miliyoyin mutanen da girgizar kasa ta shafa.
Girgizar kasar ta auku ne ranar 6 ga watan Fabrairu a larduna 11.
Girgizar kasar, mai karfin maki 7.7 da 7.6 da ta faru a kudancin Turkiyya, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 50,000 kuma ta shafi kasar Syria da ke makwabtaka.
Da yake jawabi a lardin Kahramanmaras inda girgizar ta fi yi wa illa, Erdogan ya ce gwamnati tana gina sabbin gidaje 650,000 a yankuna 11 da lamarin ya shafa.
“Mun soma da gina fiye da gidaje 105,000 kuma mun aza tubalin gina rabinsu,” a cewar Erdogan, yayin da yake jawabi a wurin bikin kaddamar da gina gidaje a lardunan Gaziantep da Kahramanmaras.
Babban abokinsa a harkar siyasa Devlet Bahceli ne ya yi masa rakiya.
“Muna gina sabbin gidaje 650,000 a yankuna da girgizar kasar ta shafa, ciki har da gidaje 507,000 da gidajen kauyuka 143,000. Mun shirya mika gidaje 319,000 a wannan shekarar sannan za mu sake inganta biranenmu,” a cewar shugaban kasar.
Shugaban Turkiyya ya kara da cewa ba gidaje kawai suke ginawa ba, yana mai cewa gwamnati tana gina makarantu da asibitoci da kasuwanni da wuraren shakatawa.
Kazalika ya ce baya ga wuraren da girgizar kasar ta shafa, gwamnatinsa tana gyara dukkan abubuwan da suka lalace a larduna 11 da lamarin ya yi wa illa.
Shugaba Erdogan ya sanar cewa bankin Ziraat zai bayar da bashin da ba ya dauke da kudin-ruwa ga manoma da makiyaya wadanda za su cigaba da zama a yankuna da girgizar kasar ta shafa, sannan za a taimaka musu su sake sayen dabbobi da abincinsu.