Wani da ake zargi da kasancewa jagoran wani gungun 'yan PKK, wanda suke ayyukansu a yankin North Rhine-Westphalia na ƙasar Jamus ya shiga hannun jami'an tsaron Turkiyya a Istanbul.
An cafke Mursel Durmaz, wanda ake sirranta sunansa da laƙabin Zeynel, a wani samamen haɗin gwiwa da Sashen Yaƙi da Ta'addanci na 'yan sandan Istanbul suka yi tare da Hukumar Leƙen Asirin Turkiyya, MIT, kamar yadda majiyar tsaro ta sanar ranar Asabar.
Bayan samun bayanan sirri game da cewa Durmaz, wanda ake zargin yana aiki a biranen Cologne da Troisdorf na yammacin Jamus, zai iso Istanbul ta jirgi, jami'ai sun tsare shi a filin jirgin sama na ƙasa-da-ƙasa na Sabiha Gokcen a Istanbul.
An ɗauki wanda ake zargin zuwa hedikwatar 'yan sandan Istanbul, inda aka yi bincike kansa. Bayan nan, alƙalin da ke aiki ya ba da izinin cigaba da tsare shi, cewar wasu majiyoyi da ba su yadda a ambace su ba saboda tsarin taƙaita magana da 'yan jarida.
Cikin shekaru 40 na ayyukanta na ta'addanci kan Turkiyya, PKK wadda Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka saka a jerin ƙungiyoyin ta'addanci, ta yi sanadiyyar halakar sama da mutane 40,000, da suka haɗa da mata, yara, da jarirai. Ƙungiyar YPG ita ce reshen PKK na Syria.