Isra'ila ta yi watsi da batun cewa ita ta kai harin, yayin da masu ruwa da tsaki da dama a duniya ke kira da a kaddamar da bincike. / Hoto: AA

Turkiyya ta ayyana makokin kwana uku a ƙasarta don taya Falasɗinu alhini bayan harin saman da Isra'ila ta kai kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar aƙallam mutum 500.

A matsayinmu na Turkiyya, muna jin ciwon wahalhalun da ƴan uwanmu Falasɗinawa ke sha," kamar yadda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanar a shafinsa na X yayin da ya sanar da wata doka ta shugaban ƙasa a ranar Laraba.

"A matsayin girmamawa ga dubban shaidanmu, waɗanda yawancinsu yara ne da fararen hular da ba su ba, ba su gani ba, mun ayyana makokin kwana uku a ƙasarmu," Erdogan ya ƙara da cewa, yana mai tunawa da Falasɗinawa fiye da 3,478 da hare-haren Isra'ila suka kashe tun 7 ga watan Okotoba.

Tun da fari majalisar dokokin Turkiyya a wata sanarwa ta haɗaka ta yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a kan asibitoci, tare da jaddada cewa kai hari kan cibiyoyin lafiya abu ne da ya saɓawa dokokin yaƙi na ƙasa da ƙasa.

Harin ya janyo Allah wadai da kakkausar murya daga Turkiyya, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga dukkan ƴan'adam da su ɗauki matakin dakatar da Isra'ila daga kai hare-haren "da ba a taɓa gani ba da mugunta a Gaza."

"Kai hari kan asibiti inda mata da yara da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba suke, babban misali ne na hare-haren Isra'ila na take hakki da darajar ɗan'adam," kamar yadda Erdogan ya wallafa a shafinsa na X.

“Kai hari a kan asibiti mummunan laifi ne. Yi wa mutanen da ke kwance suna jinya kisan kiyashi ya shallake tunani. Kai hari kan fararen hula amfani ne da dabarun ta’addanci, gaskiyar magana kenan,” kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun shi ma ya wallafa a shafinsa na X.

An ƙaryata ikirarin Isra'ila

Isra'ila ta musanta batun cewa ita ta kai harin sama, yayin da manyan masu ruwa da tsaki na duniya ke kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa don gano mai hannu a lamarin.

A hannu guda kuma, sashen binciken ƙwaf na gwamnatin Turkiyya ya ƙaryata ikirarin na Isra'ila da ta ce Hamas ne ta kai harin saman.

"Batun cewa ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ce ta kai hari kan Asibitin Al Ahli Arab ba Isra'ila ba ƙarya ne," a cewar Cibiyar Yaƙi da Labaran Ƙarya ta ƙasar a sanarwar da ta fitar ranar Talata da yamma a shafinta na X.

"Unguwar Al Zaytoun da ke arewacin Gaza waje ne da aka kashe ɗaruruwa fararen hula a kwanakin da Isra'ila ta zafafa kai hare-harenta," cibiyar ta ƙara da cewa.

"A lokacin da aka fayyace bidiyon sosai, an gano ƙarara cewa Hamas ba ta taɓa amfani da irin makakin da aka yi amfani da shi wanda ke da ƙarfin da zai iya lalata wannan wajen ba," sanarwar ta jaddada.

TRT World