Turkiyya ta aike da jiragen ruwa guda biyu zuwa Lebanon su kwaso ‘yan Turkiyya 2,000 yayin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin, a cewar jakadan ƙasar a Beirut.
Da yake magana da kamfanin dillacin labarai na Anadolu, Ali Baris Ulusoy ya ce Turkawan sun nemi a kwashe su saboda taɓarɓarewar tsaro wanda ƙaruwar hare-haren Isra’ila a Lebanon cikin makonnin nan ke haifarwa.
Ulusoy ya ƙara da cewa “a yau, jirage biyu na sojin ruwan Turkiyya sun isa gaɓar ruwan Beirut. Waɗannan jirage da za su iya ɗaukar mutum 2,000 za su kwashi ‘yan ƙasarmu su kai su gaɓar ruwan Mersin.”
Ya ce, an kuma kammala shirye-shirye na kwashe ‘yan kasar ta Turkiyya da abubuwan da suke buƙata.
Akwai Turkawa kimanin 13,000-14,000 a Lebanon, inda kawo yanzu mutum 2,000 suka nemi a kwashe su, a cewarsa.
Ofishin jakadancin Turkiyya a Beirut ya ce “ana shirye-shiryen” tsara jirage da su kwashe Turkawa da suke so su fita daga Lebanon ta sama to ko ta ruwa.
Jiragen da suka je Lebanon daga Turkiyya suna kuma ɗauke da tan 300 na kayan agaji, a cewar Ulusoy.
Daga baya Ma’aikatar Tsaron Ƙasa ta sanar da cewa jiragen biyu sun isa Lebanon. An sa jirage biyu aikin kwaso mutane da kai kayan agaji, yayin da aka sa wasu jiragen huɗu aikin yi musu rakiya da basu kariya.