Jirgin ruwa dauke da sama da tan 2,400 na kayan agajin jinƙai daga Turkiyya ya isa Sudan inda ya miƙa kaya masu muhimmanci ga ƙasar ta Afirka da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa da Yaki da Ibtila'o'i ta Turkiyya (AFAD) ce ta miƙa kayayyakin da suka haɗa da kayayyakin tsafta da tufafi da barguna da katifu da tufafi da kayan kula da lafiya ga mahukuntan Sudan a yayin wani biki da ta shirya a ranar Litinin.
Jami'an ofishin Jakadancin Turkiyya a Khartoum da wakilan Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross da ke Sudan da muƙaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan da mukaddashin Ministan Lafiya na Sudan da mukaddashin Ministan Cigaban Zamantakewa da mukaddashin Kwamishinan Agaji na Sudan ne suka halarci bikin miƙa kayan tallafin.
Kayan tallafin da suka bar Turkiyya daga tashar jiragen ruwa ta Mersin a ranar 13 ga Yuli sun hada da tan 1,996 na kayan abinci da tan 160 na magunguna da tan 128 na tufafi da tan 90 na kayan tsafta da tan 44 na kayayyakin amfanin wajen zama.
Sudan: Rikicin jinƙai da aka manta da shi
Sudan na ci gaba da fuskantar yunwa mafi muni da rikicin tsugunar da jama'a a duniya sakamakon shafe watanni 15 da aka yi ana yaƙi tsakanin dakarun sojin ƙasar da mayakan RSF ke yi.
A yayin da adadin mutanen da aka kashe a rikicin ya doshi 16,000, adadin mutuwar ya yi yawa sosai saboda rushewar tsarin kula da lafiya a ƙasar ta Arewa maso gabashin Afirka.
Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta rawaito cewar tun bayan fara yaƙin Sudan a watan Afrilun 2023, an raba sama da mutum miliyan 7.7 da matsugunansu a cikin ƙasar.
IOM ta lura da cewa sama da mutum miliyan biyu sun tsallaka iyakar ƙasar zuwa ƙasashe maƙwabta, kashi 55 daga cikin su yara ne 'yan kasa da shekaru.
UNICEF kuma ta rawaito cewa Sudan na da mafi yawan mutanen da aka raba da matsugunansu, tare da yara ƙanana miliyan biyar.
IOM ta bayyana cewa kashi 36 na mutanen da aka tsugunar sun fito ne daga babban birnin Khartoum sai kashi 20 daga Kudancin Darfur, da kashi 14 daga Arewacin Darfur.
Ofishin Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce a yayin da yanayin ke ci gaba da munana a Sudan, ana tirsasa wa mata da yara da dukkan iyali su gudu, suna barin dukkan kayayyakinsu.
OCHA sun rawaito cewar a yanzu Sudan na fuskantar "ƙarancin abinci mafi muni a cikin shekaru 20."
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya jaddada cewa daya cikin kowane mutum biyar a Sudan na buƙatar taimakon abinci cikin gaggawa a yayin da ake ci gaba da yaƙin basasar.
Ya ce "mutum 775,000 na fuskantar matsananciyar yunwa, inda miliyan 25.6 ke fuskantar yunwa daidai gwargwado.
Yunwa na barazana ga mutum miliyan uku
Eatizaz Yousif, daraktar Kungiyar Bayar da Agaji ta Kasa da Kasa ta IRC ta ce kusan rabin jama'ar kasar na bukatar agajin jinƙai saboda yaƙin da ake ci gaba da yi, kuma mutum miliyan uku na fuskantar hatsarin mutuwa saboda yunwa.
Wakilin UNICEF a Sudan Mandeep O'Brien ya ce kimanin yara ƙanana a Sudan miliyan 8.9 ne ke fuskantar matsanancin ƙarancin abinci da cututtuka.
Daraktar Zartarwa ta UNICEF Catherine Russell ta zayyana cewa Sudan na "daya daga cikin munanan wurare a ban kasa" ga yara kanana. Russell ta lura da cewar miliyoyin yara kanana na fama da karancin cimaka a Sudan.
A watan Afrilun 2023 ne yaƙi ya ɓarke a Sudan tsakanin Janar na Soji Abdul Fatah Al Burhan da Kwamandan RSF Mohamed Hamdan dagalo saboda rikici kan shigar da RSF rundunar sojin kasar.
Rikicin ya janyo mummunar matsalar jinƙai, kuma yaƙin ya yi ajalin kusan mutum 16,000 ya kuma raba miliyoyin da matsugunansu.
A ranar 29 ga Maris, Sudan ta kai ƙara gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, tana zargin Hadaddiyar Daular Larabawa da goyon bayan RSF, zargin da UAE ta musanta.