Turkiyya na jiran a shaida mata farashin da za ta sayi wasu jiragen yaƙi ƙirar Eurofighter Typhoon a ɗaya daga cikin matakan da take ɗauka na ƙarfafa rundunar sojin samanta, kamar yadda Ma’aikatar Tsaro ta Turkiyya ta tabbatar.
Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa duk da Turkiyya na bayar da fifiko wurin samar da kayayyakin tsaronta a cikin gida kamar su KAAN da HURJET da KIZILELMA da ANKA-3, ana ƙoƙarin sayo F-16 da kuma Eurofighter Typhoon domin magance wasu matsaloli na tsaro na gaggawa.
Hukumomi sun tabbatar da cewa tuni aka aika da takardun da ake buƙata na sayen jiragen yaƙin 40 ƙirar Eurofighter Typhoon zuwa ga Ma’aikatar Tsaron Birtaniya da kuma kamfanin jirgin.
Ana sa ran samun farashin nan da kwanaki masu zuwa. Haka kuma a ɗayan ɓangaren ana ci gaba da shirye-shiryen da suka kamata game da siyan jirgin. Wannan ci gaban ya zo daidai da shirye-shiryen da Turkiyya ke yi na ƙara zamanantar da rundunar sojin samanta da ƙarafafa aikinta.
Haɗakar kamfanonin Jamus da Birtaniya da Italiya da Sifaniya ne ke ƙera jiragen na Eurofighter Typhoon tare da wakilicin kamfanonin Airbus da BAE Systems da Leonardo.