Turkiyya na ta cika shekaru biyu tun bayan afkuwar mummunar girgizar kasa a gabashin kasar a ranar 6 ga Fabrairun 2023, tana mai cike da jimamin mutum 53,537 da suka mutu, da kuma 107,000 da suka samu raunuka.
Mazauna garuruwan da girgizar kasar ta shafa sun taru a dandali da misalin karfe 04:17 na dare a ranar Alhamis, lokacin da girgizar ta fara afkuwa, don tuna wa da wadanda ibtila'in ya rutsa da su.
An gudanar da tattaki cikin shiru a garuruwa da dama don girmama wadanda lamarin ya shafa.
A Pazarcik, cibiyar girgizar kasar a lardin Kahramanmaras, mazauna garin sun taru a gaban hasumiyar tsakiyar gari, tare da tunawa da jimamin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Turkiyya a ranar 6 ga Fabrairun 2023, wadda ta yi ajalin mutane 53,437 da jikkata wasu 107,000.
Mazauna garuruwan da girgizar kasar ta shafa sun taru a dandali da misalin karfe 04:17 na dare a ranar Alhamis, lokacin da girgizar ta fara afkuwa, don tuna wa da wadanda ibtila'in ya rutsa da su.
An gudanar da tattaki cikin tsit a garuruwa da dama da ibtila'in ya afku
A Pazarcik, cibiyar girgizar kasar a lardin Kahramanmaras, mazauna garin sun taru a gaban hasumiyar tsakiyar gari, tare da tunawa da jimamin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar.
A Hatay, daya daga cikin yankunan da lamain ya yi tsamari, wakilan addinai uku sun taru tare da yin addu'o'i don tuna wa da ranar.
An watsa jajayen furenni cikin tafkin Orontes a Turkiyya, domin tuna wa da wadanda suka rasa rayukansu.
A ranar 6 ga Fabrairu ne girgizar kasa mai karfin awo 7.7 da 7.6 suka afku a larduna 11 na Turkiyya da suka hada da Adana, Adiyaman, Diyarbakir, Elazig, Hatay, Gaziantep, Kahramanmaras, Kilis, Malatya, Osmaniye da Sanliurfa.
Sama da mutane miliyan 14 ne girgizar kasar ta shafa tare da wasu da dama a arewacin Syria.
Turkiyya na ci gaba da gina yankunan da girgiar kasar ta shafa
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yada sako ta shafinsa na X a ranar Alhamis yana mai girmamawa ga mutane 53,537 da suka mutu sakamakon girgizar kasar, yana addu'ar samun jin kai gare su.
Ya ce "Daga rana ta farko, mun hada kai a matsayin kasa da al'uma, muna cewa mu a dukule muke, kuma ba mu taba gajiya wa ba wajen taimaka wa yankunan da girgizar ta afku."
Ya yi alkarin ci gaba da gina yankunan, yana mai cewa za su ci gaba da aiki tukuru da jajircewa har zai kowa ya samu gidansa.
Daga baya a ranar Alhamis shugaba Erdogan zai halarci taron tuna wa da ranar a lardin Adiyaman.