Somalia da Turkiyya sun habaka dangantakarsu a 2011 bayan Shugaba Recep tayyip Erdogan ya kai ziyara mai tarihi zuwa kasar. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Somalia ya gana da Mesut Ozcan, Daraktan Kwalejin Diflomasiyya ta Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, a babban birnin Mogadishu.

A yammacin Litinin ne bangarorin biyu suka tattauna kan inganta hadin kai a muhimman bangarorin horarwar diflomasiyya da faɗaɗa ilimin jam'ian diflomasiyya.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Somalia ta fitar bayan ganawar ta ce tattaunawar ta kuma zurfafa wajen ganin an haɓaka alaƙar kwalejin Turkiyya da Cibiyar Diflomasiyya ta Somalia, da "manufar daukaka hadin kai da kuma tabbatar da musayar ƙwarewar ayyuka mafiya kyau."

Ta ce Fiqi ya bayyana matukar godiya ga Turkiyya saboda taimakon da take bai wa Somalia a ko yaushe.

Ankara ta bayar da horo ga jami'an diflomasiyyar Somalia sama da 80 a shekaru 15 da suka gabata.

Alaka ta kusa

Somalia da Turkiyya sun habaka dangantakarsu a 2011 bayan Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya kai ziyara mai tarihi zuwa kasar – ziyara ta farko da wani shugaba ya kai kasar daga wajen nahiyar Afirka a cikin shekaru 20.

Turkiyya na da alaka mai karfi da Somaliya a tarihi wadda ke bisa manufar cude-ni-in-cude-ka, inda tun 2011 Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya (TIKA) ta gudanar da manyan ayyuka sama da 150 a Somalia.

Turkiyya na da ofishin jakadanci mafi girma a Afirka da ke babban birnin Mogadishu, kuma ta gina sansanin soji mafi girma a wajen ƙasar don horar da sojojin ƙasa na Somalia.