Ministocin tsaron Turkiyya da na Somaliya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa ta tsaro da tattalin arziki don inganta dangantakar da ke tsakaninsu da zaman lafiya.
Yasar Guler na Turkiyya ya tarbi takwaransa na Somaliya Abdulkadir Mohamed Nur a Ankara a wani bikin soji da aka gudanar a ranar Alhamis.
Bayan zaman shawarwari da ɓangarorin biyu suka yi, sun kuma jagoranci taron wakilan ƙasashen biyu.
A yayin ganawar, an yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi tsaron ƙasashen biyu da na yankunansu, sannan aka sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen.
"Somaliya ta kasance wata muhimmiyar abokiyar hulɗar Turkiyya a nahiyar Afirka, mun yi ganawa mai matuƙar amfani da takwarana,'' in ji Guler bayan taron.
''A tattaunawar da muka yi, wadda ta gudana cikin yanayi mai daɗi da kuma ƙara ƙarfafa dangantakarmu, mun jaddada muhimmancin da muke baiwa ƴancin kai da kuma yankin ƙasar Somaliya,” in ji shi.
Kazalika ya yi nuni kan nasarar da Somaliya ta samu wajen kafa rundunar sojin ƙasa tare da gudunmawar kwamandojin Gorgor na ƙasar waɗanda Turkiyya ta ba su horo kana suka haɗa kai wajen baiwa matasa masu kishin ƙasarsu horo.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu matasan sun zama abin alfahari da koyi a nahiyar Afirka.
Nur ya ce dangantakar Somaliya da Turkiyya ta ƙara ƙarfi tun bayan ziyarar da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai ƙasar a shekarar 2011.
''Baya ga dangantakar da ke tsakanin ma'aikatunmu, yarjejeniyar da muka rattaba hannu a yau ta ƙunshi hadin gwiwa don yaƙi da ta'addanci da haɗin gwiwa tsakanin sojoji da fannin tattalin arzikinmu, muna ganin wannan yarjejeniya za ta taimaka wa Somaliya sosai,'' in ji shi.