Turkiyya da Masar

Turkiyya da Masar sun ce za su nada jakadunsu a kasashen biyu a wani mataki na sake kyautata dangantaka a tsakaninsu.

Sun bayyana haka ne a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar ranar Talata.

"Jamhuriyar Turkiyya da Jamhuriyar Larabawa ta Masar sun sanar da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu in da za ta kai matakin bude ofisoshin jakadanci," in ji sanarwar.

Turkiyya ta nada Ambasada Salih Mutlu Sen a matsayin jakada a Alkahira, yayin da ita ma Masar ta nada Amr Elhamamy a matsayin jakada a Ankara.

An kyautata dangantakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ne bisa matakin da shugabannin kasashen biyu suka dauka da kuma "muradin al'ummar Masar".

Tun 2013 bayan juyin mulkin da aka yi a Masar ake hulda tsakanin Turkiyya da Masar a matakin kananan ofisoshin jakadanci, lokacin da aka kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi.

Tsohon ministan wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ne jami'i na farko da ya kai ziyara Alkahira a shekara 11 lokacin ziyarar goyon baya da ta'aziyya da takwaransa na Masar Sameh Shoukry ya kawo kasar bayan girgizar kasar watan Fabrairu.

TRT World