Turkiyya da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) za su gudanar da wani muhimmin taron kasuwanci irinsa na farko a ranar 8 ga watan Yuli, kamar yadda Ministan Harkokin Kasuwanci na Turkiyya Omer Bolat da mataimakin shugaban EU suka sanar.
Bolat ya faɗa ranar Alhamis cewa Dombrovskis ya gayyaci tawagar Turkiyya zuwa Brussels don halartar wannan muhimmin taro.
Sanarwar ta biyo bayan wata ganawa da Bolat da Dombrovkis suka yi a sabon Ofishin ƙungiyar masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje ta Turkiyya (TIM) da aka buɗe a Brussels.
Bolat ya jaddada muradin bangarorin biyu na faɗaɗawa tare da sabunta hukumar kwastam wadda ke da alhakin tantance kayayyakin da ake shiga da fita da su daga ƙasashen biyu domin amfanin juna.
Ya bayyana ƙoƙarin da ake yi na magance batutuwan da suka shafi tsarin hukumar ta kwastam, tare da gudanar da muhimman tattaunawa da aiki tsakanin Turkiyya da ƙungiyar EU.
A yayin da yake bayyana jin daɗinsa kan batun soma muhimmiyar tattaunawar ta kasuwanci, Bolat ya ce: "Na yi matukar farin ciki da Dombrovskis ya ba da wannan gagarumar shawara ta soma tattaunawa kan kasuwanci tare da Turkiyya kuma mun amince da wannan tayin. Za mu yi aiki kan batutuwa da dama da suka shafi wannan shiri, sannan kusancinmu zai daɗa bunƙasa.''
Kasuwancin ƙasashen waje
Bolat ya kuma yi nuni da cewa kashi 40 cikin 100 na kasuwancin waje na Turkiyya tare da EU take yi, wanda hakan ya sa Turkiyya ta zama abokiyar kasuwancin ƙungiyar ta biyar mafi girma a Tarayyar Turai.
''Ta hanyar aiki tare da haɗin kai kan batutuwa daban-daban, za mu bunƙasa tattalin arzikinmu a bangarori da dama,'' a cewar Dombrovskis yayin da yake maraba da ra'ayin Bolat, yana mai bayyana jin daɗinsa inda ya sanar da babban taron kasuwanci da Turkiyya da za a yi.
"Turkiyya babbar abokiyar ƙawance ce ga EU, kuma hakan ya haɗa da kasuwanci, inda ribar da ake samu a tsakani ke ci gaba da haɓaka a cikin shekaru," in ji shi.
Ya bayyana muhimmiyar rawar da ƙungiyar masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ta Turkiyya ke takawa wajen inganta kasuwanci tare da maraba da buɗe sabon ofishin TIM a Brussels.
Dombrovskis ya yi nuni da cewa, kasuwancin da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kai su ga samun sama da Yuro biliyan 206 a shekarar 2023, yanayin da ya ɗaga matsayin Turkiyya zuwa babbar abokiyar cinikayyar EU ta biyar.
Kazalika ya kara da cewa, kasuwancin da ake yi a tsakani yana ƙara samar da daidaito tare da bunƙasa hada-hadar kuɗaɗe, inda kamfanonin Turkiyya suka shiga cikin sassan da ke samar da kayayyaki na Turai a fannoni kamar motoci da injina da na'urorin lantarki, sakamakon haɗakar.