Kamfanin jiragen saman Turkish Airlines ya ce ya koma da zirga-zirgar jiragensa zuwa ƙasar Syria bayan shafe tsawon shekaru 11 da dakatarwa.
A ranar Alhamis ne jirgin farko ya tashi daga Istanbul zuwa Damascus, yayin da 'yan Syria da dama suka yi ta nuna farin cikinsu da komawa ƙasarsu bayan shafe shekaru da dama suna gudun hijira.
Aƙalla mutane 350 ne suka samu damar shiga jirgin farko, inda wasu daga cikinsu ke ɗauke da tutar ƙasar Syria.
Ɗaya daga cikin fasinjojin mai suna Fatma Zehra ta shaida wa manema labarai cewa ta zo Turkiyya ne tun tana 'yar shekara 2 a duniya, kuma a yanzu tana matuƙar farin cikin komawa tare da danginta zuwa ƙasarsu ta asali inda aka haife ta.
''Ban taɓa ganin ƙasata ba, ina matukar farin cikin ganinta a karon farko. Za mu tashi ne daga Damascus zuwa Aleppo. Zan ga kakata a can,'' a cewar Zehra, wadda a yanzu take da shekaru 14.
Kimanin 'yan Syria miliyan 4 ne suka samu mafaka a maƙwabciyar ƙasar Turkiyya a lokacin yaƙin basasar.
A cewar wani fasinjan jirgin, Ahmet Kiraz, ya zo Turkiyya ne a shekarar 2012, inda ya gina rayuwarsa ta hanyar karatu da samun aiki, kuma bai taɓa tunanin komawa Syria ba.
''Mun yi tsammanin ba za mu taɓa komawa ba,'' in ji shi. Amma a lokaci da damar ta zo, mun yi farin ciki sosai. Zan koma ƙasata a jirgin farko, ji nake yi kamar ina mafarki,'' a cewar Kiraz.