Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya jaddada muhimmancin tafiyar wani jirgin sama-jannatin Turkiyya zuwa sararin samaniya a lokacin ganawarsa da Alper Gezeravci – dan sama-jannatin Turkiyya na farko wanda zai tafi a ranar Laraba.
Erdogan da Gezeravci sun gudanar da wani taro ta bidiyo a lokacin taron majalisar ministoci a ranar Talata, inda a lokacin ne shugaban na Turkiyya ya jaddada muhimmancin tafiya sararin samaniya, wanda ya ce zai taimaka wa bangaren kimiyya da kuma bayar da karfin gwiwa ga yara.
Erdogan ya bayyana cewa yana sa ran “wannan aikin zai zama sabon mafari,” inda ya ce: “Za mu ci gaba da wannan aikin. Za mu ci gaba da neman abu mafi girma.”
"Muna godiya gare ku da kuka bude labulen da ya takaita burinmu ga al'ummar da ke tafe," in ji Erdogan a tattaunawarsa da Gezeravci da tawagarsa.
Alamar ci gaban Turkiyya
Za a tura Gezeravci tashar sararin samaniya a daya daga cikin “aikin tafiya ta farko,” wanda shi ne karon farko na aikin Turkiyya a sararin samaniya.
Tawagar ta Turkiyya za ta tafi tashar sararin samaniyar da misalin 01:00 na dare agogon Turkiyya a ranar 18 ga watan Janairu.
Gezeravci da shirin na Axiom za su tafi a cikin rokar SpaceX Falcon 9 daga Hukumar NASA da ke Florida. Ana sa ran tawagar za