Tashar TRT mallakin gwamnatin Turkiyya, ta ƙaddamar da sabon sashen watsa labarai na dijital na harshen Sipaniya, wato TRT Español a yayin wani taron Watsa Labarai na Ƙasashen da ke magana da harshen Sifaninyanci na Farko na TRT.
"Muna fatan TRT Español za ta kasance mai amfani gare mu da kuma kasashen da ke magana da harshen Sifaniya," in ji daraktan sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun, yayin da yake jawabi a bikin kaddamar da tashar a Istanbul ranar Juma'a.
Altun ya ƙara da cewa sashen wani bangare ne na manufofin Turkiyya na inganta bai wa harsuna da yawa damar bayyana manufofi masu kyau, inda ya sha alwashin cewa, "kafofin yada labaran Turkiyya za su ci gaba da yaƙi da zalunci da kuma bayar da murya ga wadanda ake zalunta."
Shi ma Darakta Janar na TRT Mehmet Zahid Sobaci ya yi jawabi a wajen taron, inda ya ce TRT Español ta samar da wani sabon zamani ga Turkiyya a Latin Amurka da Sifaniya.
"Daga Spain zuwa Latin Amurka, Turkiyya na inganta dangantakarta a yankin," in ji shi, ya ƙara da cewa TRT na kara ƙarfafa dangantaka da masu watsa shirye-shirye a can.
A karkashin taken "The Place Where People Matter," "Wurin da mutane ke da mahimmanci," TRT Espanol na da nufin hade bangarorin al'adu guda biyu cikin hangen nesa da samar da sahhan labarai da gabatar da al'amuran duniya.
An samar da tashar don masu magana d aharshen Sifaniyanci
A ranar Alhamis ne aka fara taron watsa labarai na ƙasashe masu magana da harshen Sipaniya tare da wani taron ƙara wa juna sani na ‘yan jarida daga kasashen da ke magana da harshen Sifaniya.
Taron wanda aka yi wa laƙabi da "Aikin jarida na ƙasa da ƙasa," ya mayar da hankali ne kan batutuwa kamar aikin jarida na rashin son-kai da muradun jama'a da dangantakar diflomasiyya da tasirin siyasar kafofin watsa labarai da ƙarfafa tattaunawa da musayar ra'ayi.
A ranar Juma'a da rana kuma za a tattauna a kan batutuwan kamar: "Karfafa Fahimtar Juna Ta Hanyar Fina-Finai Masu Dogon Zango: Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci," "Alakar Turkiyya da Kasashen da ke magana da Yaren Spaniyanci ta Fuskar Kafafan Yada Labarai: Manufar Bai-Daya da Kabulabale a Nan Gaba," da kuma "Sauyawar Samun Labarai a Duniya: Habaka Muryoyin Kasashe masu magana da Yaren Sifaniyanci don Fahimtar Duniya da Adalci."
Tashar TRT Español za ta dinga samar da labarai da shirye-shirye na musamman ga masu magana da yaren Spaniyanci, yaren da ake magana da shi a kasashe sama da 20 a duniya.
Dama tuni akwai sassan TRT na TRT Francais da TRT Balkan mai watsa shirye-shirye a yaruka uku da kuma TRT Afrika mai yaruka huɗu.