Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu shi ne mutum na karshe da zai yi magana a kan duk wani abin da ya shafi kisan kare dangi, a cewar Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Fahrettin Altun.
"Netanyahu ya ƙware wajen sayar da duniya da amfani da laifuffukan yaƙi da ya yi a kan fararen hula a matsayin kare kai. Duk da cewa duniya ta kasa hana shi, tarihi zai hukunta shi a matsayin wanda ya aikata laifin yaƙi,” ya fada a shafinsa na X a ranar Laraba.
Da yake tabbatar da cewa Netanyahu shi ne "mutum na karshe da ya yi magana game da gwagwarmayar da muke yi da ta'addanci", Altun ya jaddada cewa Turkiyya shafe fiye da shekaru 40 tana yaƙi da kungiyar ta'addanci ta PKK da kuma rassanta.
“Su kansu Kurdawa a Turkiyya sun yi yaƙi da PKK da ke kashe fararen hula da kananan yara ba gaira ba dalili kamar yadda Netanyahu ke yi!,” Altun ya ƙara da cewa.
Da yake jaddada cewa Netanyahu "shi ne mutum na ƙarshe da zai yi magana game da ɗabi'a," Altun ya soki Firaministan Isra'ilan kan shekarun da ya shafe kan aniyarsa ta korar Falasɗinawa daga yankunansu.
"A yanzu kuma ya sauya salon hakan ta hanyar amfani da sojin Isra'ila wajen kashe fararen hula a gidajensu da asibitoci da kuma sansanonin ƴan gudun hijira," ya faɗa.
Daraktan sadarwar ya sake nanata kiran da Turkiyya ta yi ga al'ummar duniya da su yi aiki tare don ganin an tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da yin kira da a gudanar da shawarwarin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Altun ya kara da cewa Ankara za ta ci gaba da yin hakan ba tare da la'akari da hare-haren siyasa da cin mutuncin da ake yi wa Turkiyya ba. Za mu ci gaba da fadin gaskiya!