A shekarun bayan nan, Baykar ya samar da fiye da kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta daga jiragen yaki marasa matuka take fitarwa / Photo: AA Archive

Italiya ta amince da sayar da katafaren kamfanin zirga-zirgar jiragen samanta na Piaggio Aerospace, ga kamfanin ƙera jiragen sama na yaƙi marasa matuƙa na Turkiyya da ke ƙera jirage samfurin UCAV na Baykar.

"Babban kamfanin ƙera jirage samfurin UCAV Baykar ya yi nasara a kan takwarorinsa da dama a fadin duniya da suka nemi sayen kamfanin Piaggio Aerospace, wanda aka samar da shi a shekarar 1884," a cewar Baykar cikin wata sanarwa da ya fiytar a ranar Juma'a kan batun amincewar, wadda ta fito daga Ma'aikatar Masana'antu ta Italiya.

Baykar na aiki da kamfanin Pragma Consulting a kan batun cinikin da ma sauran batutuwa.

Piaggio Aerospace ya yi fice a masana'antar jiragen sama ne wajen samar da jiragen kasuwanci samfurin P.180 Avanti da aka fi sani da Ferrari a sararin samaniya, da kuma samar da injinanjiragen sama.

Kamfanin yana kuma taka muhimmiyar arwa a masana'antar tsaro ta Italiya saboda yadda yake gyara da inganta harkokin jiragen sama, kuma an san shi da irin gudunmawar da yake bayarwa a fannin fasaha na Italiya a tsawon shekara 140 a tarihi.

A sanarwar da ya fitar, ministan masana'antu na Italiya Adolfo Urso ya ce an sake ƙaddamar da kamfanin ne domin cim ma muradun jiragen sama.

"Bayan shekara shida ana jira, muna miƙa kamfani mai muhimmanci na ƙasarmu Piaggio Aerospace, don burin samar da tsari mai muhimmanci da inganta shi a dogon zango," in ministan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a yanzu Baykar zai ƙara ƙarfafa tasirinsa a kasuwar jiragen sama ta Turai, tare da adana tarihin kamfanin Piaggio mai muhimmanci da inganta tsarin ƙere-ƙerensa.

Ta ce: "Wannan lamari zai ƙara samar da damarmakin samun ayyuka a Baykar kamar yadda Piaggio ke yi a Italiya."

"Wannna mataki mai muhimmanci ya ƙara darajta nasarar harkokin sufurin saman Turkiyya da kuma tabbatar da cewa tarihin Piaggio ya ci gaba da wanzuwa a cikin yarjejeniyar."

A shekarar 2023, an sanya Baykar a cikin manyan kamfanoni 10 na Turkiyya da suka fi fitar da kayayyakinsu ƙasashen waje a dukkan fannoni, inda ya samar da dala biliyan 1.8 a fitar da kayayyaki.

Wani rahoto na wata cibiyar bincike kan tsaro da ke Amurka, Center for a New American Security, Turkiyya ce ke da kashi 65 cikin 100 na jiragen yaƙi marasa matuƙa samfurin UAV da ake fitarwa wasu ƙasashe, inda Baykar kadai ke da kashi 60 cikin 100 - nunki uku kan abin da Amurka ke fitarwa.

A shekarun bayan nan, Baykar ya samar da fiye da kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta daga jiragen yaki marasa matuka da take fitarwa, inda ta fitar da samfurin Bayraktar TB2 UCAVs da Bayraktar AKINCI UCAVs zuwa ƙasashe 35.

TRT World