Taken taron na bana shi ne "Bunkasa hanyoyin Diflomasiyya a lokutan rikici". / Hoto: antalyadf.org

A watan gobe ne za a gudanar da Taron Diflomasiyya na Antalya inda shugabannin ƙasashe fiye da 20 tare da jami'ai daga sama da ƙasashe 100 za su halarta, a cewar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Oncu Keceli ya sanya wa hannu ta ce za a gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tsakanin 1- 3 ga watan Maris.

Kimanin ministoci 90 ne za su halarci taron, da suka haɗa da ministocin harkokin waje fiye da 60, sai kuma wakilan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 80.

Keceli ya bayyana cewa kimanin baƙi 4,000 da suka haɗa da ɗalibai ne ake sa ran za su halarci taron, wanda a yayin gudanar da shi za a yi taruka kashi-kashi har zuwa hamsin inda za a tattauna kan batutuwa da dama.

A yayin taron, za a gudanar da wata tattunawa, inda ƴan ƙungiyar "Gaza Contact Group" za su haɗu.

Taron, wanda aka soma yin sa tun 2021, zai gudana ne a wani ƙasaitaccen wajen shaƙatawa na Antalya da ke gaɓar teku.

Taken taron na bana shi ne "Bunƙasa hanyoyin Diflomasiyya a lokutan rikici."

AA