Shugaba Erdogan ya tattauna da takwaransa na Indonesiya Joko Widodo, da na Koriya ta Kudu da Australiya. Hoto/AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya hadu da shugabannin duniya da dama ciki har da shugaban Japan Fumio Kishida kan batun farfado da yarjejeniyar fitar da hatsi ta Tekun Bahar Rum a lokacin da ake taron G20 a New Delhi na Indiya.

Shugaba Erdogan ya tattauna da shugabannin MIKTA, wanda hadin gwiwa ce ta kasashen Mexico da Indonesia da Koriya ta Kudu da Australia.

A lokacin tattaunarwsu wadda suka garkame kofa, Erdogan da shugaban Japan sun tattauna kan dangantakar kasashen Turkiyya da Japan ta fannoni daban-daban.

Haka kuma sun tattauna kan lamuran yankuna da duniya baki daya wadanda suka shafi kasashen, kamar yadda sasashen watsa labarai na Turkiyya ya bayyana.

A lokacin da yake tattaunawa da Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, Shugaba Erdogan ya yi wa shugaban Brazil fatan alheri wanda shi ne zai karbi jagorancin G20 a shekarar 2024.

Ya bayyana cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fannin kasuwanci da cinikayya wadda ke kan dala biliyan 5.6 a bara za ta iya karuwa zuwa dala biliyan 10 idan aka hada kai.  

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan da Ministan Baitulmali da Kudi Mehmet Simsek da Shugaban Leken Asiri na Turkiyya Ibrahim Kalin da Daraktan Watsa Labarai Fahrettin Altun da babban mai ba shugaban kasa shawara kan Akif Cagatay Kilic da Hasan Dogan duk suna daga cikin tawagar da Shugaba Erdogan ya tafi da ita Indiya.

Baya ga tattaunawar da Shugaba Erdogan ya yi da shugabannin MIKTA, ya kuma ja gefe ya tattauna da takwaransa na Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol.

Indiya na karbar bakuncin taron kwanaki biyu na G20 mai taken “Duniya daya, al’umma daya, makoma daya,” inda shugabannin G20 baya ga Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban China Xi Jinping da ba su halarci taron ba, za su tattauna a taruka uku, inda suke sa ran samun ci gaba ta fannin kasuwanci da sauyin yanayi da wasu matsaloli da duniya ke fuskanta.

Firaiministan Indiya Narendra Modi ya yi maraba da Shugaba Erdogan a daidai lokacin da ya isa zauren taron domin taron ranar farko. A rana ta farko shugabannin za su gudanar da taro.

A rana ta biyu kuwa za su je kabarin Mahatma Gandhi domin ajiye furanni a kabarinsa kafin daga bisani su wuce wurin taron shuka itatuwa.

Turkiyya ta dauki wannan taron na G20 da matukar muhimmanci sakamakon taron yana hada kasashen da suka ci gaba da kuma masu tasowa wuri guda.

Hakan na nufin kasar na goyon bayan matakan ci gaba na G20. Turkiyya ta karbi bakoncin shugabannin duniya a Nuwambar 2015 a lardin Antalya da ke kudancin kasar a lokacin da kasar ke da shugabancin G20.

TRT World