Shugaban Turkiyya Erdogan ya miƙa gaisuwar Sallah ga al'ummar duniya . / Hoto: AA Archive

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da saƙon Babbar Sallah ranar Lahadi, inda ya yi addu'ar neman kwanciyar hankali da nutsuwa a ƙasar da ma 'yan'uwa Musulmai da ke faɗin duniya.

"Ina taya murna ga ƙasarmu da ƙasashen duniya game da bikin Babbar Sallah wato Eid al Adha," kamar yadda ya bayyana a shafin X.

Ya ƙara da cewa,"Ina taya murnar Babbar Sallah ga 'yan'uwana da ke Gaza waɗanda ke bukukuwan Sallah yayin da suke fama da kisan kiyashi daga Isra'ila. Kuma ina fata 'yan'uwanmu da ke shan wahala da waɗanda ake yi wa danniya da waɗanda ake yi wa kisan kiyashi kullum za su samu kwanciyar hankali da tsaro nan ba da jimawa ba."

Babbar Sallah, ko kuma Sallar Layya, lokaci ne na tunawa da Annabi Ibrahim (AS) game da biyayyar da ya yi wa Allah yayin da ya ba shi umarnin yanka ɗansa.

Tun da farko, a Ranar Arafat, Erdogan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga Falasɗinawa waɗanda suke gudanar da Babbar Sallah a lokacin da Isra'ila take ci gaba da yi musu kisan kiyashi.

Tun ranar 7 ga watan Oktoban bara, Turkiyya take sukar Isra'ila kan hare-haren da take kai wa Gaza da kuma mamayar da take yi wa Falasɗinu, wanda ake kallo a matsayin kisan ƙare-dangi.

Turkiyya ta aika da kayan agaji fiye da tan dubu 55 zuwa yankin Gaza.

TRT World