Mutane sun yi addu'o'i a Masallacin Sualtan Ahmed (The Blue Mosque) lokacin murnar Maulidin Annabi SAW, wanda ake yi domin murnar kewayowar watan haihuwar Manzon Allah SAW a birnin Istanbul.  / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aika da saƙon fatan alkhairi saboda zuwan Maulidin Annabi Muhammad SAW, yana bayyana fatan cewa maulidin zai kawo kwanciyar hankali da albarka, ba ga Musulmi kaɗai ba, har ma ga duka 'yan adam.

"A wannan lokaci na musamman da ake murnar kewayowar watan haihuwar Annabi, ina ƙara nuna girmamawa ga masoyinmu Annabi Muhammad, jagoranmu kuma shugabanmu, da cikakkiyar mutuntawa da ganin girma," kamar yadda ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ranar Asabar.

"Ina addu'a da fatan daren Maulidin ya kawo alkhairai da albarka ga Musulmai da duniya baki ɗaya."

Musulmai a faɗin duniya suna yin bikin Maulidin Annabi SAW a ranar 12 ga watan Rabi-ul-Awwal, inda ranar ta bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, saboda bambancin lokaci.

A lokacin maulidin, Musulmai na yin abubuwa da dama na nuna farin ciki, da suka haɗa da karatun Alƙur'ani, da addu'o'i, da halartar wuraren jawabai dangane da rayuwar Manzon Allah SAW da koyarwarsa, da gudanar da tarurruka da raba abinci.

Ana bayar da hutun ranar a ƙasashe da dama da Musulmai ke da rinjaye, da suka haɗa da Pakistan da Indonesia da Malaysia da Bangladesh da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da wasu bangarori na Indiya.

TRT World