Shugaba Erdogan ya ce Turkiyya za ta ci gaba da yin kowane ƙoƙari don tabbatar da zaman lafiya da yankin. Hoto: AA Archive

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Vladimir Putin kan ta’azzarar da rikicin Isra’ila da Falasdinu ke yi da kuma tabarbarewar halin jinkai a yankin.

A cewar Ma’aikatar Watsa Labarai ta Turkiyya, Erdogan ya shaida wa Putin cewa cin zalin da ake yi a kasar Falasɗinu yana ƙaruwa kuma ana ci gaba da kashe Falasɗinawa a duk minti guda.

Shugaban ƙasar Turkiyya ya ce yin “shirun ƙasashen Yamma na ta’azzara bala’in jinƙai a Gaza zuwa wani mataki,” ma’aikatar ta faɗa a shafin X.

Ya bayyana cewa Turkiyya za ta ci gaba da yin kowane ƙoƙari don tabbatar da zaman lafiya da yankin.

Rikicin Gaza, inda Isra'ila ke kai hare-hare da sanya ƙawanta tun ranar 7 ga watan okrtoba, ya fara ne a lokacin da ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa ta ƙaddamar da wasu hare-hare tab sama da ta ƙasa da ta ruwa a kan Isra'ila.

Ta ce ta yi hakan ne a matsayin martani ga yawan afka wa Masallacin Ƙudus da Isra'ila ke yi da kuma kai wa Falasɗinawa hare-hare.

Daga nan sai rundunar sojin Isra'ila ita ma ta ƙaddamar da ahre-haren ramuwa a kan yankunan Hamas a Gaza.

An kashe fiye da mutum 7,100 a rikicin, da suka haɗa da Falasɗinawa 5,791 da kuma Isra'ilawa 1,400.

Caccakar Kwamitin Tsaro na MDD

Shugaba Erdogan ya kuma zargi Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da rura wutar rikicin ta hanyar "bin bayan gwamnatin Isra'ila."

"Kasashen duniya ba sa tashi tsaye wajen fuskantar kalubalen da ake fuskanta musamman a yanayin da Isra'ila ke cin zarafin fararen hula, lamarin da ya saba wa doka," a cewar Erdogan a wata sanarwa.

"Kwamitin Tsaron na rura rikicin ta hanyar bin bayan bangare daya maimakon dakatar da kashe fararen hula," Shugaba Erdogan ya ƙara da cewa.

AA