Erdogan ya fitar da sabbin tsare-tsare da busharori ga 'yan kasar a 'yan kwanakin nan/ Hoto TRT World

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa gwamnati za ta kara yawan albashin ma’aikatan gwamnati wanda mafi karanci zai kama Lira 22,000 ($1,124).

A yayin jawabinsa a ranar Alhamis a Ankara, Shugaba Erdogan ya ce “Za mu tsara mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnati, wanda ba zai zama kasa da mafi karancin albashin ma’aikatan jama’a ba. A watan Yuli, mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnati zai kama Lira 22,000.”

Erdogan ya kara da cewa wannan karin albashi zai kuma shafi ‘yan fansho. Na umarci ministanmu da ya kammala wannan aiki nan da watan Yuli.”

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaba Erdogan ya sanar da karin kashi 45 na ma’aikatan jama’a su 700,000, inda mafi karancin nasu albashin ya kama Lira 15,000 ($768).