A ranar 17 ga watan Yuli Rasha ta dakatar da yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine wadda aka soma a Fabrairun 2022. Hoto/AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa birnin Sochi na Rasha domin tattaunawa da takwaransa Vladimir Putin.

A yayin ziyarar tasa wadda ya kai a ranar Litinin, ana sa ran Shugaba Erdogan zai tattauna kan matsalolin yanki da na duniya baki daya, da kuma dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Rasha.

Ana kuma sa ran shugabannin za su tattauna kan yarjejeniyar fitar da hatsi wadda ta taimaka aka magance karancin abinci amma a halin yanzu yarjejeniyar ta kawo karshe kuma ba a sabuntata ba.

Bayan da Rasha ta dakatar da yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine wadda Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka shiga tsakani wurin kulla ta, Ankara na ta kokari domin dawo da yarjejeniyar.

Moscow ta yi korafi kan cewa kasashen Yamma ba su cike sharudan da ya kamata ta fannin fitar da hatsin, haka kuma babu isashen hatsin Ukraine da yake zuwa kasashen da ke bukata.

Rashar ta bayyana cewa takunkumin da aka saka kan biyan kudi da jigila da inshora sun kasance kalubale wurin fitar da hatsin.

Da take tabbatar da muhimmancin biyan bukatun kasar Rasha na fitar da hatsi da takinta zuwa kasashen waje, Turkiyya ta ce babu wani zabi da ya wuce wannan.

TRT World