Sojojin Isra'ila ne suka harbe Aysenur Ezgi Eygi a lokacin da ake zanga-zanga dangane da Yahudawa 'yan kama wuri zauna a garin Beita da ke gundumar Nablus ta Gabar Yamma da Kogin Jordan. / Hoto: Others

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira kan a gudanar da "cikakken bincike" a bayyane dangane da kashe wata 'yar Turkiyya kuma 'yar Amurka mai gwagwarmayar neman zaman lafiya wadda sojojin Isra'ila suka kashe a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

"Muna so mu ga an gudanar da cikakken bincike dangane da abin da ya faru da kuma hukunta waɗanda ke da hannu," kamar yadda mai magana da yawun MDD ɗin Stephane Dujarric ya bayyana a wani taron manema labarai a ranar Juma'a, bayan an samu labarin cewa 'yar gwagwarmayar ta rasu sakamakon raunin harbin binidgar da ta samu bayan sojojin na Isra'ila sun harbe ta.

"Dole ne farar hula, a kare su a kowane lokaci," kamar yadda ya ƙara da cewa.

Ko da aka tambaya ko akwai wani bincike da aka yi dangane da wasu daga cikin jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da Isra'ila ta kashe, sai Dujarric ya ce: "Ba mu ga wani abu ba."

A lokacin da yake bayyana cewa za a gudanar da bincike "da zarar an kammala yaƙin," Dujarric ya bayyana cewa akwai wani "ɗan ci gaba" dangane da duba batun cin zalin da ake yi wa Falasɗinawa da ake tsare da su.

'Kai hari dagangan'

Sojojin Isra'ila sun harbe Aysenur Ezgi Eygi a ranar Juma'a a yayin wata zanga-zangar nuna adawa da matsugunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna na Isra'ila a garin Beita da ke gundumar Nablus a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

Eygi, wadda aka haifa a birnin Antalya na kasar Turkiyya a shekarar 1998, ta rasu ne sakamakon raunukan da ta samu duk da yunkurin da kungiyoyin likitoci suka yi na farfaɗo da ita, a cewar Fouad Nafaa. daraktan asibitin Rafidiya.

Waɗanda suka shaida lamarin sun sanar da cewa, sojojin Isra'ila sun bude wuta kai tsaye kan wasu Falasdinawa da suke gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da haramtattun matsugunan Yahudawa da ke tsaunin Sbeih da ke Beita a kudancin Nablus.

Jonathan Pollack, wanda ya shaida kisan kuma wani dan gwagwarmayar Isra'ila da ya shiga zanga-zangar adawa da 'yan kama wuri zauna na Isra'ila ya ce, ya ce sojan da ya harbe Eygi "yana kallonta ƙirƙiri a gabansa."

"Yana da muhimmanci a gare ni in ce wannan ba wani lamari ne keɓantacce ba," in ji Pollack, inda ya kara da cewa tun daga shekarar 2021, an kashe mutum 17 a zanga-zangar da ake yi a Beita, wadanda dukkansu Falasdinawa ne.

"Wannan wani bangare ne na ƙara faɗaɗa da Isra'ila ke yi a Yammacin Gabar Kogin Jordan a 'yan watannin nan kuma wani bangare ne na kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza."

Kungiyar hadin kan kasa da kasa da Falasdinu ke jagoranta (ISM) ta kuma ce da gangan sojan na Isra'ila ya harbi Eygi, inda ta kafa hujjarta da wata shaida wadda wata da take wurin mai suna Mariam Dag (ba sunanta na asali ba) ta bayar wadda ita ma 'yar aikin sa kai ce ta ISM

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta ce kisan Eygi "sakamakon aiwatar da umarnin" 'yan siyasar Isra'ila ne na kashe Falasdinawa da masu fafutuka.

Ma'aikatar ta ɗora wa gwamnatin Isra'ila alhakin wannan aika-aika wanda ya tabbatar da shirinta na ta'azzara lamarin domin gudanar da ayyukanta na mulkin mallaka a yankunan da ta mamaye.

TRT World