Ankara ta amince da halaccin Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libiya. / Hoto: AA Archive

Turkiyya na goyon bayan sulhun kasa da kawo karshen rikicin siyasar da ya sake bayyana a Libiya da ke arewacin Afirka a watan da ya gabata bayan da majalisar dokoki ta dakatar da wa'adin gwamnatin da kasashe duniya suka amince da ita mai hedkwata a Tarabulus.

A wata ziyara zuwa Tarabulus a ranar Alhamis, shugaban hukumar leken asiri ta Turkiyya Ibrahim Kalin, ya gana da manya shugabannin Libiya inda ya jaddada muhimmancin kauce wa wani sabon rikici a kasar.

Kalin ya gana da shugaban gwamnatin Hadin Kan Kasa da ke Tarabulus, Abdulhamid Dbeibah, da Abdullah al Lafi da Mossa al Koni na Majalisar Shugaban Kasa, kamar yadda wata sanarwa da Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta sanar.

Ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga zaman lafiya da hadin kan Libiya, yana mai bayyana fatan cewa rarrabuwar kan siyasar zai wuce ta hanyar tattaunawar sulun kasa.

Kalin da Dbeibah sun tattauna kan alakar kasashensu, cigaban yankunansu, batutuwan manufofin bai daya da halin da ake ciki yanzu haka a Gaza da ke Falasdin. Su biyun, sun bayyana bukatar hada kai a bangarorin siyasa da tsaro, tallafa wa zaman lafiya kasa da kare fararen hula.

Shugaban na MIT ya kuma gana da mahukunta daga Majalisar Kasa, wasu ministoci da manyan jami'an tsaro da na leken asiri.

Tsakanin majalisar dokoki da Tarabulus

Ankara ta amince da halacin Gwamnatin Hadin Kasa ta Libiya, kuma tana ci gaba da goyon bayan kokarin tattaunawa da manufar dabbaka cikakken goyon baya ga kasar da yaki ya daidaita.

A watan da ya gabata, Majalisar Wakilai ta Libiya ta jefa kuri'ar zabar aiki da majalisar ministoci ta Gabashin Libiya karkashin Osama Hammad tare da cewar ita ce "halastacciyar gwamnatin kasa har sai an sake zabar sabuwar gwamnatin hadin kan kasar".

Majalisar dokokin ta kuma sanar da sunan shugabanta, Aguila Saleh, a matsayim kwamandan rundunar sojin Libiya, maimakon Majalisar Shugaban Kasa.

Tun 2011 Libiya ta fada rikici, a loakcin a aka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Gaddafi da ya yi mulki na tsawon shekaru 40.

A yanzu bangarori biyu da ke hamayya da juna ne ke shugabantar kasar: Gwamnatin Hadin Kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita da Dbeibah ke jagoranta a Tarabulus, wadda ke da iko da yammacin Libiya, da gwamnatin Osama Hammad, wadda majalisar dokoki ta kafa, kuma take gudanar da mulki a Benghazi, tana jagorantar gabashi da kudancin Libiya.

A 2020, Turkiyya ta tura dakaru zuwa Libiya don goyon bayan gwamnatin Hadin Kan Kasa. A matakin da aka dauka watanni tara da suka gabata, kasar ta kara wa'adin zmaan sojojin Turkiyya a Libiya har nan d 2026, tana mai gargadin cewa hatsarin da ke fito wa daga Libiya na shafar Turkiyya da dukkan yankin.

TRT World