A  karkashin sabuwar yarjejeniyar, jiragen saman da ke kai komo tsakanin Turkiyya da Masar su 30 za su karu zuwa 67 a cikin mako guda. / Photo: AA

Adadin jiragen saman da ke kai-komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu sama da ninki guda, in ji Ministan Sufuri da Gina Ƙasa na Turkiyya a ranar Alhamis.

A karkashin sabuwar yarjejeniyar, jiragen saman da ke kai komo tsakanin Turkiyya da Masar za su karu daga 30 zuwa 67 a cikin mako guda, in ji sanarwa ta Abdulkadir Uraloglu.

A gawanar da aka yi a ranar Laraba a yayin Taron Hadin Kai na Kasashen Biyu a babban birnin Ankara na Turkiyya karkashin shugabancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi, an sanya hannu kan yarjeniyoyi a bangarorin sufurin jirgin kasa, da fasahar sadarwa da sufurin jiragen sama.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasa daga Masar ya ziyarci Turkiyya a cikin shekaru sama da 10, yunkurin wani bangare na Turkiyya na inganta alakarta da makotanta da ke gabar tekun Bahar Rum.

TRT Afrika