Bikin wannan shekarar na tunawa da ayyana Turkiyya a matsayin Jamhuriya, da ake yi a ranar 29 ga watan Oktoba kowacce shekara, yana da ma'ana ta zahiri.
Da yake nuni da cikar jamhuriyar shekaru 100 da samuwa, bikin tunawa da ranar, wani muhimmin abu ne da zai bayar da damar yin waiwaye game da inda Jamhuriyar ta jaddada ƴancin kanta da kuma muradanta na ci-gaba tsawon lokaci, da kuma inda ta nufa nan gaba.
Idan aka duba tarihi, Ataturk ya bayyana sunan ƙasar a hukumance, sannan ya ayyana matsayinta a matsayin Jamhuriya ranar 29 ga watan Oktoba, a shekarar 1923.
Daga bisani, an kaɗa ƙuri'a a babbar Majalisar Dokoki Ta Ƙasa, kuma an zaɓi Ataturk babu hamayya a matsayin shugaban kasar Jamhuriyar Turkiyya na farko.
Tun daga nan, Turkiyya na gudanar da BIkin Ranar Jamhuriya kowace ranar 29 ga watan Oktoba na kowace shekara a faɗin duka gundumomin ƙasar da ma a ƙasashen ƙetare.
Bikin na bana zai mayar da hankali ne a kan shika-shikan ci-gaba da aka shimfiɗa tare da ginshiƙin Jamhuriyar.
Ga bayanai a kan muhimman ci-gaba da aka samu a waɗannan shekaru ɗarin:
Gudanar da zaɓuɓɓuka
Na gaba gaba daga cikin nasarorin da aka samu, shi ne shimfiɗa tsarin Dimokuraɗiyya, wanda ya fuskanci ɗimbin ƙalubale a baya, daga juyin mulkin sojoji zuwa haramta jam'iyun siyasa da kuma batu na wakilci a majalisar dokoki ta ƙasa.
Ƙasar ta yi ƙoƙari wajen gudanar da galibin zaɓuɓuka bisa tsarin Dimokuraɗiyya, biyo bayan komawa ta farkin tsarin Shugabanci mai jam'iyu da yawa a shekarar 1950.
Zuwa watan Maris na shekarar 2023, lokacin da aka gudanar da jerin zaɓuɓɓuka na baya bayan nan a Turkiyya, adadin jam'iyun siyasa ya ƙaru zuwa 126.
Bambance-bambance a wakilci na siyasa
Bayan an bai wa mata cikakken ƴancin damawa da su a siyasa a shekarar 1934, girman wakilcinsu a majalisar dokoki ta ƙasa, ya kai inda bai taɓa kaiwa ba, inda aka samu mata ƴan majalisar dokoki guda 121.
Yayin da aka rage adadin shekaru mafi ƙaranci da mutum zai iya tsayawa takara, zuwa shekara 18 da haihuwa, a shekarar 2017, shigar ƴan takara matasa cikin majalisar dokoki ta Turkiyya, har ila yau, ya nuna bambanci shekaru da ke tsakanin ƴan majalisar.
Bugu da ƙari, adadin masu kaɗa ƙuri'a da ke fitowa zaɓe ya ƙaru sosai. A zaɓen shugaban ƙasa na baya bayan nan, an samu adadin masu kaɗa ƙuri'a kashi 87.05 a zagayen farko, da kuma kashi 84.15 a zagaye na biyu.
Tabbatar Da Tsarin Shugaban Ƙasa Da Kuma Dokar Ƙawancen Siyasa
A ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta 2017, an sauya tsarin Firaminista zuwa na shugaban ƙasa mai cikakken iko, biyo bayan wani yunƙuri da aka yi tun a baya, na hukumantar da tsarin mafi rinjaye su zaɓi shugaban ƙasa. A shekarar 2021, an amince da dokar ƙawancen siyasa, da ke bai wa ƙananan jam'iyu dama su yi taron dangi ko su ƙulla ƙawance. Hakan ya taimaka wa waɗannan jam'iyun, ƙetare ƙa'idar samun kashi 7%, kafin samun cancantar shiga zaɓen, wacce ita kanta ƙa'idar, rage ta a ka yi daga kashi 10%. Gabaɗayansu, waɗannan matakan, su suka yi sanadin samun bambance-bambance a fagen siyasa, yayin da Turkiyya ke cika shekaru 100 cif cif da zama Jamhuriyya.
Mota mai amfani da wutar lantarki ta farko: TOGG
Jamhuriyar Turkiyya mai cike da daidaiton siyasa ta share hanyar samar da ƙirƙire ƙirƙiren fasaha a ɓangaren motoci, da tsaro da kuma makamashi. Ƙarfafa ƴancin kan ƙasar Turkiyya, ƙirƙire ƙirƙire sun yi silar samun nasarori da dama a fagen ƙasa da ƙasa. Burin Turkiyya na tsawon shekaru 60, mota mai amfani da wutar lantarki ta farko, TOGG, an ƙaddamar da ita a shekarar 2019, abin da ta zama wata gagarumar alamar cigaban ƙasar a fannin fasahar zamani.
Gagarumin ci-gaba a fannin tsaro da kuma ƙaruwar tsaro
Wani ɓangaren da Turkiyya ta samu gagarumin cigaba a ƙoƙarin da take yi na zama mai dogaro da Kai, shi ne a wajen samar da ingantattun matakan yaƙi da ta'addaci da kuma fasahar zamani, ta hanyar ƙera jirage marasa matuƙa samfurin UAVs da UCAVs da kuma fitar da su waje.
A shekaru Ashirin da suka wuce, Sashen tsaro na Turkiyya ya rage dogaron da yake yi da ƙasashen waje daga kashi 80% zuwa kashi 20%. Yanzu, a cikin ƙanƙanin lokaci, Turkiye, har wa yau, ta samar da irin waɗannan kayan daban daban.
Akwai samfurin Bayraktar TB-3, Kizilelma, jirage marasa matuƙa samfurin Akinci, jiragen yaƙi masu masu saukar angulu, jiragen ruwa na yaƙi, tamkar yaƙi jirgin yaƙi, na'urorin kakkaɓo jirage, yayin da jirgi mara matuƙi samfurin TCG Anadolu tuna yana cikin jerin kayayyakin da Jamhuriyyar Turkiyya za ta nuna a bukinta na cika shekaru 100th da zama Jamhuriyya.
Bayan ta zamanantar kuma ta inganta rundunonin tsaronta, Turkiye ta samu gagarumar nasara a yaƙi da take yi da ta'addacin na ƙungiyoyin PKK/YPG, inda a baya bayan nan, ta yi nasarar kai hari kan ƙungiyoyin ƴan ta'adda a Arewacin Iraqi da Arewacin Syria.
Shirin Kula da sararin samaniya na ƙasa
Har wa yau, Turkiyya ta kafa Hukumar Kula Da Sararin Samaniya Turkiyya a shekarar 2018, sannan ta ƙaddamar da shirinta na kula da sararin samaniya a shekarar 2019. Ta ƙaddamar da Tauraron Ɗan adam Mai Sa Ido A Doron Ƙasa IMECE, nata na gida, a duniyar wata, ta ci gaba da bincikenta da kuma nazari kan gano abubuwa.
Wadataccen Makamashi da Zuba jari a hanyoyin samar da makamashi mai tsafta
A ƙoƙarinta na zama muhimmiyar mai cin gashin kai da dogaro da kai, Turkiyya ta ƙara yawan gano makamashi, da bincike da kuma wasu aikace-aikacen atisaye a Bahar Aswad, kuma a karon farko,ta tura gas da aka samu a gida daga Bahar Aswad zuwa cikin cibiyar makamashinta ta gida.
Domin raba ƙafa a fanninta na albarkatun makamashi, har ila yau, Turkiyya ta zuba jari a fannin makamashi mai tsafta sannan ta fara gina cibiyar makamashin nukiliya a Mersin.
Zuwa watan Oktoba na wannan shekarar, Turkiyya ta samar da megawat 11,602, na makamashi da ake samu daga iska, yayin da kuma take ƙaddamar da cibiyarta ta tara iska ta farko da ke kan teku.
Ta duk shirye shiryenta na samar da tsaftataccen makamashi, yanzu adadin tsaftataccen makamashin da Turkiyya ke amfani da shi, yana matsayin na biyar a nahiyar Turai kuma na goma sha biyu a duniya.
Aikin Gona
A matsayinta ta ɗaya daga cikin masu samar da abinci mafi muhimmanci a duniya, Turkiyya ta tabbatar da samar da wadataccen abinci akai akai, a cikin shekaru 100 na tarihin jumhuriyyar.
Ƙasar ta yi amfani da ƙirƙire ƙirƙire na fasahar zamani a fannin, sannan ta fito da wasu manufofi da suka rage tafiya ci-rani daga yankunan karkara zuwa birane, yayin da kuma ake ƙarfafa samar da abinci a cikin gida.
Bayan ta yi ta faɗi-tashi, musamman a shekaru ashirin ɗin da suka gabata, fannin aikin gona na Turkiyya, a yanzu, yana ɗaya daga cikin guda 10 mafi girma a duniya. Amfanin kayan gona ya samu tagomashi na samar da dala biliyan $56 shekarar 2022 daga dala biliyan $24.48 a 2002.
Waɗannan alƙaluma sun nuna a ƙaruwar fitar da kayayyaki ƙasashen ƙetare, wanda ya kai matsayin da bai taɓa kaiwa ba, na samar da dala biliyan $34.2 a shekarar 2022.
Aikin Jirgin Ƙasa
Tsawon tarihinta na shekaru 100, Jamhuriyyar ta zuba jarin maƙudan kuɗi wajen gina hanyoyin jirgin ƙasa. Daga kilomita dubu 7,671 km a shekarar 1950, hanyoyin sun faɗaɗa zuwa kilomita dubu 10,940 km a shekarar 2002, suka kai kilomita dubu 13,919 km a shekarar 2023.
Daga shekarar 2002, hankula sun koma kan hanyoyin jiragen ƙasa masu ɗan karen gudu, inda kawo yanzu,an gina kilomita 2,251 km.
Iraqi ta ɓullo da sabon shiri mai suna "Developmen Road" da zai haɗa da layin dogo mai nisan kilomita 1,200 km da kuma hanyar mota kwatankwacinta, da za ta haɗe ƙasar da Turkiyya. Sashen sufurin zai amfani yankuna masu faɗi, daga yankin Persia zuwa Turai.
Bututan mai
Ƙari a kan waɗannan hanyoyin da ke haɗe biranen Turkiyya da yawa, an shimfiɗa bututaye da yawa domin gudanar da jigilar mai da iskar gas da sauran hanyoyin samar da makamashi.
Daga Azrabijan zuwa Turkiyya da Turai, daga Georgia zuwa Turkiyya, daga Russia zuwa Turkiyya, daga Iraqi zuwa Turkiyya - waɗannan bututayen sun ƙarfafa hanyar samar da wadataccen makamashin ƙasar, yayin da kuma suke bayar da gudummawa wajen haɗin kai kan makamashin da kuma bayar da tabbacin samar da makamashi wa kasuwanni ƙasashen duniya.