Shugaba Erdoğan ya ce yana sa rai “duka kungiyoyin kwallon kafa su rungumi tsarin wasan gaskiya da gaskiya. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa amfani da wasannin motsa jiki domin cimma wata manufa ta siyasa “ba zai amfanar da komai ba”, bayan an daga wani wasa mai muhimmanci da aka yi niyyar bugawa tsakanin Fenerbahce da Galatasaray inda aka ce an daga shi ne sakamakon wasu dalilai na shirye-shirye.

“Mayar da wasanni a matsayin wata hanya ta siyasa a kullum, kan ko wane irin dalili, ba daidai bane, kuma ba shi da amfani,” kamar yadda Erdogan ya shaida a lokacin da yake yin bayani a taron bayar da kyaututtuka na Necip Fazil wanda aka gudanar a birnin Santambul a ranar Asabar.

“Muna son wasannin Turkiyya musamman kwallon kafa, su haskaka ba ta hanyar jayayya ba, amma ta hanyar nasara,” kamar yadda ya kara da cewa.

Shugaban na Turkiyya ya bayyana cewa yana sa rai “duka kungiyoyin kwallon kafa su rungumi tsarin wasan gaskiya da gaskiya, da kuma samar da zaman lafiya da hadin kai a bangaren wasannin.

Jawabin Erdogan din na zuwa ne kwana guda bayan an dakatar da wasan karshe na Turkish Super Cup tsakanin Galatasaray da Fenerbahce wanda aka shirya bugawa a Riyadh.

TRT World