Shugaba Recep Tayyip Erdogan bai taba faduwa zabe ba tun shekarar 1994. Ga abin da ya mayar da shi gagarabadau a siyasa.
Turkiyya za ta gudanar da zabuka a tsakiyar watan Mayu, lokacin da za a gwada farin jinin Shugaba Erdogan, mai shekaru 69, wanda zai fuskanci dan takarar shugaban kasa na gamayyar ‘yan hamayya.
Tun lokacin da aka zabe shi a matsayin Magajin Birnin Istanbul a 1994, Erdogan bai taba faduwa zabe ba ko da sau daya. Kuma a tarihinsa sau biyu kacal ya taba faduwa zabe, sa’ilin da ya yi takararsa ta farko a shekarun 1980.
Ranar 14 ga watan Mayu za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisu. Erdogan, wanda ya lashe zabukan shugabancin kasa a 2014 da 2018, yana neman zama shugaban Turkiyya na 13.
Yana takara ne karkashin ‘Kawancen Al’umma’, wadda gamayya ce ta Jam’iyyun AK da Nationalist Movement Party (MHP) da BBP, da Yeniden Refah Party, da kuma HUDA PAR.
Erdogan da magoya bayansa ne suka kafa Jam’iyyar AK Party bisa turbar ra’ayin mazan jiya na dimokuradiyya a 2001.
A shekarar da ta biyo baya, jam’iyyar ta samu gagarumin rinjaye a Majalisar Dokoki, a wata irin nasara kan jam’iyyun da aka saba da su masu ra’ayin tsakiya.
Wannan nasara ta Erdogan ta share fagen zuwan sabon salon siyasa karkashin Shugaba Erdogan.
A shekarar 2002, kalilan cikin masu sharhi ne suka yi hasashen Erdogan da Jam’iyyarsa ta AK Party za su yi ta yin nasara ba kakkautawa.
Kuma ba su yi tunanin zai samu isasshen karfin siyasa da har zai sauya tsarin gwamnatin kasar daga na firaminista zuwa na shugaba mai cikakken iko ba. Hakan ya faru ne bayan zaben raba-gardama na shekarar 2017.
Ba bata lokaci Shugaba Erdogan ya kaddamar da manufofinsa na siyasa, har ya gina kasar da a yau take zuba jari a nahiyar Afirka, kuma take taka rawa wajen warware rikice-rikice kamar na Ukraine, da Azerbaijan, da Libiya, da Siriya.
Ya kuma habaka fannonin tsaron kasa da na makamashi.
Sabanin yawancin shugabannin siyasa a kasashen yammacin duniya wadanda suka gina shuhurarsu bisa tsarin dimukuradiyyar da hamshakan mutane ke jagoranta, Erdogan ya fara ne daga matsayin gama-garin mutane.
Ya fito ne daga al’ummar gama-gari ta Turkiyya, wadanda suke fama da takaicin dankwafe alamun addini da ra’ayin rikau, karkashin masu akidar Kemalism da ke da tsattsauran ra'ayin ba ruwanmu da addini.
Tushen siyasar Erdogan
An haifi Erdogan a Guneysu, wani lardi mai duwatsu da ke gundumar Rize ta gefen Bahar Aswad. Ya girma a yankin saboda mahaifinsa kyaftin ne a rundunar Tsaron Iyakokin Ruwa ta Turkiyya.
A shekarar 1960, iyayensa sun yi kaura zuwa Kasimpasa da ke Istanbul, wata unguwa ta masu karamin karfi. Rayuwa a wannan unguwa ta yi tasiri a zuciyar matashi Erdogan.
Kasimpasa tana yankin Golden Horn na Istanbul, wato Halic, wanda yake kunshe da mutane iri-iri.
Erdogan ya sayar da lemon zaki da biredin simit a titunan Kasimpasa. Ta haka ne ya samu fahimtar rayuwar yau da kullum ta gama-garin mutanen Turkiyya, inda ra’ayin mazan jiya yake cakuda da mararin lokacin Daular Usumaniyyar Usmaniyya.
Tun yana yaro ya fara sha’awar kwallon kafa, da kuma siyasa. Yana daf da shiga babbar kungiyar nan mai farin jina a Istanbul, ta Fenerbahce, sai babansa ya nuna adawarsa da zabin shiga kwallon kafa.
Sakamakon haka Erdogan ya zabi shiga harkar siyasa gadan-gadan.
A shekarar 1981, Erdogan ya kammala karatu a fannin Gudanar da Kasuwanci, a Makarantar Nazarin Tattalin Arziki da Kimiyyar Kasuwanci, wadda aka sauya wa suna zuwa sashen nazarin tattalin arziki na Jami’ar Marmara.
Erdogan ya shiga sahun ‘yan fafutukar Milli Gorus ta National Vision, wadda aka fi ganin Necmettin Erbakan ne ya kafa, wanda injiniya ne mai kishin addini.
Erbakan da abokansa sun kafa Jam’iyyar National Salvation Party (MSP) a shekarar 1972, a zaman reshen siyasa na Milli Gorus.
Ajandar siyasar ‘yan fafutukar Milli Gorus ya dogara ne kan tunanin cewa, Turkiyya a matsayinta na kasa mai rinjayen al’ummar Musulmai, za ta iya zama mai fada a ji, ta hanyar dabarun cigaban tattalin arziki kan tsarin hikimar kasuwanci ‘yan Anatolia, kuma ba tare da ta saryar da martabar Musulunci ba.
A shekarar 1976, Erdogan ya zama shugaban reshen matasa na jam’iyyar
Sakamakon kazamin juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 1980, Erdogan ya ci gaba da bin tafarkin Erbakan, har ya zamo shugaban reshen Istanbul na sabuwar Jam’iyyar Welfare Party a shekarar 1985.
Bayan rashin nasara sau biyu na zamowa Magajin Garin Beyoglu, da zamowa dan majalisa mai wakiltar Istanbul, ya cimma wani matsayi a harkar siyasarsa a shekarar 1994.
Magajin garin Istanbul
Lokacin da Erdogan ya yi takara a zaben karamar hukuma a birnin Istanbul, inda ya ja da manyan ‘yan siyasa masu sassaucin ra’ayi, yawancin ‘yan takarar sun raina takararsa, suna ganin ba yadda za a yi dan takarar Welfare Party ya ci zabe.
Sai da ta kai har masu gabatar da shirye-shiryen siyasa suka ki gayyatarsa, saboda ba sa ganin yana da wata damar cin zabe.
Amma a safiyar 27 ga watan Maris, Erdogan ya lashe zaben, abin da ya girgiza manyan gwamnatin da sojoji ke shugabanta, saboda suna kallon Welfare Party a matsayin barazana ga fahimtarsu ta akidar kauracewa addini, wadda a lokacin har ta kai ga haramta hijabi a jami’o’i.
Erdogan ya nuna hazakarsa a zangon mulkinsa na magajin gari, inda ya yi maganin manyan matsalolin Istanbul, har da matsalar dauke ruwan famfo, da ta sufuri, da ta gurbatar yanayi da kwashe shara.
Matsalolin sun haifar da yaduwar sinadarin methane a gundumar Umraniye ta bangaren Asiya na garin Istanbul a shekarar 1993, lokacin mulkin tsohon magajin garin mai ra’ayin sauyi.
Haka nan ya yi nasarar aiwatar da shirin tsaftace yankin Golden Horn, wanda gabar tekunsa take unguwar da ya girma ta Kasimpasa.
Sai dai tasirin Erdogan bai fito ba sosai sakamakon tsattsauran ra’ayin akidar ba ruwanmu da addini, irin salon akidar ‘laicism’ ta Faransa, wadda ke neman gwamnati ta kula da ra’ayoyin addini.
Wannan tsari na akidar ba ruwanmu da addini ya saba wa salon Ingila, wanda ke kare sassaucin tsarin raba siyasa da addini.
A shekarar 1999, an yanke wa Erdogan hukuncin wata biyar a gidan kaso saboda ya rera waken marubuci mai akidar kishin kasa, Ziya Gokalp, wanda ra’ayoyinsa suka taimaka wa uban kasar Turkiyya Mustafa Kemal Ataturk.
Hukuncin wanda na makarkashiya ne, ya haramta wa Erdogan shiga harkokin siyasa, wanda ya tilasta masa barin mukaminsa na magajin gari.
Hukuncin ya bai wa masu ra’ayin mazan jiya mamaki, da kuma mazauna Istanbul, wadanda suka shaida cigaban rayuwa a zamanin mulkinsa. Hakan ya janyo wa Erdogan sabon farin jini.
A shekarar 2013, lokacin yana firaminista, Erdogan ya ziyarci gidan kason da ya taba zama, a Pinarhisar wadda take Kirklareli, wani lardi a yankin Turkiyya na bangaren Turai da ake kira Thrace.
Erdogan ya ce, Pinarhisar gare ni shaida ce ta sabuwar rayuwa, a inda muka shirya kafa Jam’iyyar AK. A can ne muka dauki takun farko na kafa sabuwar Turkiyya mai daraja.
Shugaban Turkiyya
Shekara biyu bayan sakinsa daga gidan yari, Erdogan da masu ra’ayi irin nasa sun samu lakabin “masu son sauyi”, sabanin ragowar mabiya tsagin Erbakan, wadanda aka yi wa lakabi da “yan gargajiya”.
Erdogan da mutanensa sun kafa Jam’iyyar AK bayan darewar Jam’iyyar Virtue, wadda ta gaji jam’iyyar Welfare Party wadda aka haramta.
Ta hanyar kafa AK Party, Erdogan na da manufar jan ra’ayin duka masu sassaucin ra’ayin mazan jiya, da masu akidar kishin kasa, har ma da ‘yan ra’ayin sauyi masu sassuci, wadanda suka bar asalin tafiyar Milli Gorus ta Erbakan.
Amma Erdogan ya ci gaba da girmama gwagwarmayar Erbakan har zuwa lokacin mutuwar dattijon. Erdogan ya yaba da abin gajiyar da ya bar wa ‘yan baya.
A shekarar 2002, dabarun Erdogan sun tabbata wani sabon salon siyasa, yayin da jam’iyyarsa ta ci zabe, ta kayar da jam’iyyun gargajiya na kasar, tare da wagegiyar tazara.
Tun bayan nan, Erdogan ya ci zaben kasa inda ya zamo Firaminista a shekarar 2007 da 2011, sannan da zaben shugaban kasa sau biyu, a 2014 da 2018, inda ya zamo shugaban kasar Tukiyya.
Daga 2002 zuwa yau, jam’iyyarsa ta lashe zabuka uku na raba-gardama kan sauye-sauyen tsarin mulkin kasa, wadanda suka hada da sauya tsarin gwamnati daga na firaminista zuwa na shugaba mai cikakken ‘yanci.
Jam’iyyar Erdogan ta samu rinjaye a zauren majalisa, a duka zabuka tun daga 2002. Hakan wani tarihi ne da ba jam’iyyar da ta taba kafawa, tun komawar Turkiyya tsarin jam’iyyu masu yawa a 1950.
A karkashin mulkinsa, rawar da soji suke takawa a sha’anin siyasar kasar ya ragu matuka, yayin da gwamnatin farar hula ta samu karin karfi.
Gabanin mulkin Erdogan, hukumomin sojin kasar sun barar da zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya a 1960, da 1980, da 1997. Juyin mulkin da ya yi nasara a baya-bayan nan shi ne na salon juyin mulkin zamani, wanda ya sauke gwamnatin Erbakan a 1997.
A watan Yuli na 2016 an yi yunkurin juyin mulkin da wasu tsirarun sojoji da ke bin koyarwar Fethullah Gulen, jagoran kungiyar ta’adda ta Fethullah Terrorist Organisation (FETO) da ke zaune a Amurka.
An ci galaba kan masu yunkurin bayan da shugaba Erdogan ya yi kira ga al’ummar kasa masu kishin dimikuradiyya su yaki masu yunkurin juyin mulkin a kan titunan kasar.
Yunkurin juyin mulkin ya yi sanadin salwantar daruruwan rayuka da raunata dubban mutane da suka tirje. Gabanin yunkurin, FETO ta yi amfani da haramtattun hanyoyi suka mamaye hukumomin gwamnati, da nufin karbe iko da turakun siayasar kasar.
Duk da cewa Erdogan yana da masu sukarsa a ciki da wajen Turkiyya, salon shugabancinsa na gina Turkiyya ta zama kasa mai cikakken ‘yancin dogaro da kanta, ya sanya ya gwanance wajen kulla kawance da sauya alkiblar siyasa a Turkiyya da ma sassan duniya.
Sakamakon wannan, bayan sauya alkiblar tarin manufofin gida da waje na kasarsa, salon jagorancinsa ya janyo masa masoya a Turkiyya da ma cikin shugabannin duniya, daga Ukraine, zuwa Rasha, zuwa Afirka, da kasashen Asiya, da kasashe masu rinjiyen al’ummar Musulmai.
A zabukan ranar 14 ga watan Mayu, Erdogan yana da burin ci gaba da rike mukamin shugaban kasa, da kare manufofinsa na siyasa.
Sannan yana fatan jam’iyyarsa da kuma kawancensu na ‘People’s Alliance, su ci gaba da rike rinjaye a majalisar dokoki.
Biyo bayan mummunar girgizar kasar da aka yi a Turkiyya a watan Fabrairu, wadda ta kashe dubban mutane a Turkiyya, za a saurari ganin ko zaben wannan shekara zai yi wa Erdogan sauki kamar zabukan baya.