Kawancen jam'iyyu na Shugaba Erdogan ya samu 'yan majalisa mafi yawa. Hoto/ REUTERS

Zaben da aka yi na Turkiyya a ranar 28 ga watan Mayu ya bayar da wani kyakkyawan yanayi na siyasa ga Shugaban kasar wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa.

Erdogan bai fadi zabe ba tun 1994, a lokacin da aka zabe shi magajin garin Istanbul. A yanzu bayan ya samu nasara a zabe zagaye na biyu, shugaban ya kara kafa tarihi.

Akwai dalilai da dama da suka sa Erdogan ya samu nasara kan kawancen jam’iyyu shida na dan takarar CHP Kemal Kilicdaroglu, amma ga wasu daga cikin muhimmai daga cikinsu da suka sa ya kayar da da 'yan hamayya a duka zagayen zaben.

Kwarewa da iya hada kai

Tun lokacin da Turkiyya ta koma kan tsarin jam’iyyu fiye da biyu a shekarun 1950, babu shugaban kasa da ya ci zabuka masu yawa kamar Erdogan, kuma wannan wata manuniya ce ta siyasa da ta kara nuna irin kwarewa da kuma bambancinsa da sauran abokan adawarsa ta siyasa.

Sai dai kuma Kilicdaroglu mai tsattsauran ra’ayi wanda ke jagorantar bangaren adawa na jam’iyyu shida, ana kallonsa a matsayin dan takara mara karfi idan aka kwatanta shi da Erdogan.

Ba kamar bangaren adawa ba, Erdogan ya hada wani kawance na masu kyakkyawan ra’ayi na ‘yan mazan jiya na addini da kuma kishin kasar Turkiyya, jam’iyyu biyu masu ra’ayi da ya zo daya, wanda suka hada kan jam’iyyun Nationalist Movement Party (MHP) da Buyuk Birlik Party (BBP) da kuma Yeniden Refah Party, inda suke da akida kusan iri daya.

Kafin tafiya zagaye na biyun, a wata siyasa da aka buga, Erdogan ya hada kai da Sinan Ogan, wanda dan takarar shugaban kasa ne da ya ci sama da kashi biyar na kuri’u a zagaye na farko, inda ya goyi bayan Erdogan.

A dayen bangaren, a wani mataki mai sarkakiya da ya dauka, Kilicdaroglu sai ya cimma matsaya da shugaban masu tsananain tsatsauran ra’ayin nan Umit Ozdag domin tattaro kuri’un magoya bayansa daga jam’iyyar Zafer da niyyar wuce kuri’un Erdogan.

Masu sharhi sun yi tunanin cewa matakin da Kilicdaroglu ya yi zuwa tsananin tsatsauran ra’ayi ya kara hada kan masu ra;ayin kawo sauyi da kuma kuri’un Kurdawa duk da cewa HDP wadda ke da alaka da ‘yan ta’addan PKK sun ci gaba da goyon bayansa.

HDP din na samun akasarin goyon bayanta daga Kurdawa wadanda akasari ke kudu maso gabashi da kuma gabashin kasar.

Daidaita lamuran cikin gida

Duka zabukan ‘yan majalisa da na shugaban kasa da aka gudanar sun nuna wa shugaban mai mulki da kawayen jam’iyyunsa wata hanya, inda ta nuna cewa jama’ar Turkiyya sun yarda da tsare-tsaren Erdogan.

A lokacin yakin neman zaben, Erdogan ya yi alkawarin ci gaba da daidaita lamuran siyasa ta hanyar ci gaba da matakan yaki da ta’addanci.

A dayen bangaren kuma, kawancen Kilicdaroglu mai rauni ya goyi bayan HDP da ke da alaka da PKK, lamarin da ya kara jefa masu zaben Turkiyya cikin fargaba, inda masu zaben suke kallon shugaban masu tsatsauran ra’ayin a matsayin wanda ba shi da karfin da zai iya yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Yarjejeniyar fitar da hatsi. Hoto/AA

Tsare-tsaren harkokin waje

Mulki mai tsawo na Erdogan ya kara damar Turkiyya a siyasance ta zama daya daga cikin kasashen duniya masu karfin iko a daidai lokacin da Amurka ke kara rasa karfi a kasashen duniya da kuma irin ikon da take da shi a Gabas ta Tsakiya da Tsakiyar Asia.

Erdogan ya yi matukar kokari wurin shiga tsakani a wurare da dama da ake rikici da suka hada da Libiya da Ukraine inda yake kare muradan Turkawa a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kara karfin siyasar Turkiyya a tsakiyar Asia da Turkiyyar ke da fada a ji.

A yakin Ukraine, Turkiyya ta zama mai shiga tsakani inda ta jagoranci yarjejeniyar hatsi tsakanin Kiev da Moscow kuma hakan ya yiwu ne sakamakon kyakkyawar alaka tsakanin Erdogan da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da kuma Volodymyr Zelensky na Ukraine.

Shiri bayan girgizar kasa

A ranar 6 ga watan Fabrairu, kudancin Turkiyya ya gamu da girgizar kasa biyu masu karfi, wadanda suka jawo mutuwar sama da mutum 500,000 da kuma barin larduna da dama a lalace.

Amma Erdogan ya yi matukar kokari wurin tattara duk kayayyakin agaji na Turkiyya domin tallafa wa yankunan da girgizar kasar ta shafa.

Ba lallai bane wani dan siyasar Turkiyya ya samu irin wannan nasarar, kamar aiwatar da shirin samar da gidaje 650,000.

Yadda Erdogan yake yawan zuwa wuraren da girgizar kasar ta shafa ya sa mutane suka gane cewa Erdogan zai iya taimakon wadanda girgizar kasar ta shafa fiye da duk wani dan siyasa.

Samar da makamashi

A karkashin mulkin Erdogan, Turkiyya ta yi kokarin gano hanyoyin makamashi da ba a taba amfani da su ba a gabashin Bahar Rum da Bahar Aswad, inda Turkiyya ta kara kulla alaka mai karfi da kasashe masu samar da gas kamar Rasha da kasashen yankin Gulf.

Sabon gas din wanda aka gano a cikin teku, Turkiyya tana ganin zai ishe ta tare da kawarta Turkish Republic of Northern Cyprus.

Sakamakon hakan, Turkiyya ta kaddamar da wani shiri na bincike a yankin, inda ta rinka gasa da kasashe kamar Girka da Isra’ila domin nuna wa jama’a cewa Turkiyya za ta iya hako gas dinta a gabashin Tekun Mediterranean.

Masana na cewa akwai gas kwance da ya kai cubic metres tiriliyan 3.45 da gangar mai biliyan 1.7, kamar yadda masana suka bayyana.

A Bahar Aswad, Turkiyya ta kara aikin da take yi na tono gas, inda ta samu kusan cubic meter biliyan 600 a rijiyoyin Sakarya da suka hada da Tuna-1 zuwa Amasra-1 da Caycuma-1 tun daga 2020.

“Idan muka fada aiki gadangadan, za mu iya samar da kashi 30 cikin 100 na abin da kasarmu ke bukata a duk shekara daga wadannan rijiyoyi,” in ji Erdogan, inda ya kara da cewa bai kai shekara uku da Turkiyya ta soma bayar da gas din ta gano ga ‘yan kasa ba.

“Za mu tona cubic meter miliyan 10 ta gas a kullun daga rijiyar da ke Sakaraya a karon farko sa’annan nan gaba cubic meter miliyan 40 a duk rana daga sabbin rijiyoyin da za mu tono a nan gaba,” in ji shi.

TRT World