Mevlut Cavusoglu / Photo: AA

Ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya yi tsokaci game da zaben shugaban kasa a Turkiyya, wanda za a yi ranar 14 ga watan Mayu.

Ministan ya ce “Muna da zabe a gabanmu. Yanzu muna gudanar da zabe duk shekara biyar a Turkiyya. Wannan na nufin cikakken aminci da zaman lafiya.”

Da yake jawabi ranar Juma’a, ministan ya bayyana cewa Turkiyya ta samu nasarori masu yawa a gida da waje, karkashin mulkin jam’iyyarsu ta AK Party. Ya bayyana hakan ne a wani taro da magoya bayan jam’iyyar a jihar New Jersey da ke Amurka.

Minista Cavusoglu ya jaddada batun “zaman lafiya” a kasar Turkiyya a karkashin jam’iyyar Adalci da Cigaba, wato AK Party.

Ya bayyana hakan ne a gaban wata tawaga ta ’yan sa-kai na AK Party’, a garin Paterson, wanda yake da yawan ‘yan asalin Turkiyya.

Minista Cavusoglu ya janyo hankalinsu kan jerin cigaban da kasarsu ta samu a mulkin jam’iyyar.

Cavusoglu ya soki lamirin wasu shugabannin jam’iyyu a Turkiyya, wadanda suke cewa za su mayar da kasar tsohon tsarin kulla kawance.

Ya kara da cewa, “Mutane ba za su aminta da wannan ba. Suna so su mayar da Turkiyya zuwa zamanin rudu. Wannan batu shi ya kara mayar da zaben nan mai matukar muhimmanci”.

Yayin jawabinsa ga ‘yan Turkiya wadanda za su yi zabensu a Amurka, inda za su fara daga 29 ga watan Afrilu, ya ce a karkashin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, Turkiyya ta cimma manyan muradunta na cikin gida da na waje, a cikin lumana.

Har wa yau, Minista Cavusoglu ya bayyana cewa shekaru 20 da suka gabata, Turkiyya ta dogara kan kasashen waje don samun kashi 80 na kayan yaki da take bukata. Amma yanzu abin ya sauya.

A yau Turkiyya tana kera makamai masu kyau sama da wadanda take yi a baya, har tana sayar da su ga kasashen waje na kimanin dala biliyan 4.5.

Ministan ya gode wa Turkawa mazauna Amurka bisa tallafin da suka bayar bayan aukuwar girgizar kasar da aka yi a Turkiyya ranar shida ga watan Fabrairu.

Ya kara da cewa, "Mun samu gagarumin tallafi daga ‘yan kasarmu da ke zaune a Amurka bayan wannan ibtila’in”.

Ministan harkokin wajen na Turkiyya ya je Amurka ne don halartar taro kan muhalli, na “International Zero Waste Day” a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma hadu da mai dakin shugaban Turkiyya, wato Emine Erdogan.

TRT World