Ana sa ran shugaban Rasha Vladimir Putin zai ziyarci kasar Turkiyya ranar 27 ga watan Afrilu, don ayyana tashar makamashin ta Akkuyu a matsayin tashar nukiliya, a cewar Shugaba Recep Tayyib Erdogan.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce akwai yiwuwar takwaransa Vladimir Putin zai kawo ziyara Turkiyya ranar 27 ga watan Afrilu don kaddamar da tashar nukiliya ta farko a kasar, wadda aka gina tare da hadin gwiwar kamfanin makamashin nukiliya na gwamnatin Rasha, wato Rosatom.
“Shugaba Putin zai iya zuwa Turkiyya ranar 27 ga Afrilu domin halartar bikin kaddamarwar. Ko kuma mu halarci taron ta intanet,” a fadin Shugaba Erdowan ranar Laraba, yayin wata zantawa da gidajen jaridar Turkiyya na A Haber da ATV. “Muna fatan za mu dauki wannan mataki na farko.”
Shugaba Erdogan ya ce Tashar Makamashin Nukiliya ta Akkuyu wani “gagarumin shiri” ne, inda ya kara da cewa tashar za ta taimaka wa kasar wajen “adana makamashi da gaske”.
Tashar Akkuyu, wadda ake kan ginawa a halin yanzu a yankin kudancin lardin Mersin, za ta zamo tashar nukiliya ta farko a kasar.
Injin sarrafa nukiliya na farko zai fara aiki a wannan shekara ta 2023, yayin da gaba dayan tashar za ta kammalu ta fara aiki a shekarar 2025.
An soma shirin gina tashar ne bayan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatocin Turkiyya da Rasha.
An shirya tashar za ta kasance mai mizanin aiki don samar da wuta megawat 4,800, da injin sarrafa nukiliya guda hudu.
An kuma tsara tashar ta fara samar da wutar lantarki nan gaba cikin wannan shekarar.